logo

HAUSA

Sojojin Kamaru sun hallaka mayakan Boko Haram 20

2021-07-27 10:06:47 CRI

Sojojin Kamaru sun hallaka mayakan Boko Haram 20_fororder_210727-saminu 1-Kamaru

Wata majiyar sojojin kasar Kamarun da ta nemi a boye sunanta, ta bayyana cewa, a kalla mayakan kungiyar Boko Haram 20 sun gamu da ajalinsu, lokacin da ’yan Boko Haram din suka kaddamar da hari kan wani sassanin soji dake yankin arewa mai nisa, a ranar Asabar din karshen makon jiya.

A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar sojojin Kamarun kanal Didier Badjeck ya fitar a jiya Litinin, sojoji 8 sun rasu, kana wasu 13 sun jikkata lokacin dauki ba dadin da ya auku tsakanin sassan biyu.

Badjeck ya kara da cewa, "Sojojin Kamaru na cikin shirin ko ta kwana, a yankin arewa mai nisa da sauran sassan dake wajen kan iyakar Kamaru, inda suke aiki ba dare ba rana, domin dakile duk wani hari daga mayakan na ’yan ta’addan Boko Haram masu yawaita kaddamar da farmaki.

Shi ma gwamnan yankin Midjiyawa Bakari, ya ce mayakan Boko Haram na kara matsa kaimin kaddamar da hare-hare kan sansanonin sojoji dake yankin, tun bayan mutuwar tsohon shugabansu Abubakar Shekau.   (Saminu)