logo

HAUSA

An mika wa wata makarantar kasar Jamus wasikar da Madam Peng Liyuan ta rubuta

2021-03-01 21:41:53 CRI

Bayan da aka dade ana dakatar da karatu sakamakon annobar cutar COVID-19, makarantar Burggymnasium ta kasar Jamus, ta farfado da darasi a kwanakin baya. Sa’an nan wasu jami’an gidan jakadancin kasar Sin dake kasar Jamus sun ziyarci makarantar, musamman ma domin mika wa malamai da daliban makarantar wasikar da Madam Peng Liyuan, uwargidan shugaban kasar Sin Xi Jinping ta rubuta musu. A cikin wasikar, Madam Peng ta karfafa wa malamai da dalibai na makarantar gwiwarsu, domin su samar da karin gudunmawa ga kokarin yaukaka zumunta tsakanin jama’ar kasashen Jamus da Sin.

Madam Peng ta taba ziyartar makarantar a shekarar 2014. (Bello Wang)

Bello