logo

HAUSA

Xi Jinping ya gabatar da rubutaccen jawabi ga babban taron hadin gwiwar kasa da kasa a yankin Asiya da Fasifik kan "Ziri daya da hanya daya"

2021-06-23 21:11:01 cri

Yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da rubutaccen jawabi ga babban taron hadin gwiwar kasa da kasa, na yankin Asiya da Fasifik kan "Ziri daya da hanya daya".

A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, ya gabatar da raya shawarar "Ziri daya da hanya" cikin hadin gwiwa ne, da nufin ciyar da ruhin hanyar siliki gaba, da yin kokari tare don gina dandalin hadin kai budadde, da samar da sabon karfin gwiwa ga hadin kai, da ci gaba a tsakanin kasashe daban daban.

A cewar Xi Jinping, a cikin shekaru 8 da suka gabata, kasashe 140 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa tare da kasar Sin, don raya shawarar "Ziri daya da hanya" tare. (Bilkisu)