Ministan harkokin wajen kasar Sin zai halarci taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin G20
2021-06-28 19:43:57 CRI
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana Litinin din nan cewa, dan majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, zai halarci taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar G20 da zai gudana ta kafar bidiyo.
Ya kara da cewa, Wang Yi zai halarci taron ne bisa gayyatar takwaransa na kasar Italiya Luigi Di Maio, za kuma su tattauna batutuwa kamar cudanyar bangarori daban-daban, da tsarin tafiyar da harkokin duniya da sauran mahalarta taron.(Ibrahim)
Labarai Masu Nasaba
- Wang Yi ya halarci liyafar ranar Afirka da aka shirya a Beijing
- Wang Yi zai jagoranci taron kwamitin sulhun MDD kan rikicin Isra’ila da Palestine
- Ministan harkokin wajen Sin ya bayyana matsayar Sin kan rikicin Falastinawa da Isra’ila
- Kasar Sin Za Ta Hada Hannu Da Sauran Kasashe Wajen Dakile Annobar COVID-19