logo

HAUSA

Shugabannin Sin Amurka sun cimma ra'ayi daya kan batutuwa da yawa

2017-11-10 17:12:08 CRI

Bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa, shugaban kasar Amurka Donald Trump yana ziyarar aiki a kasar Sin da ga ranar 8 zuwa ta 10 ga watan da muke ciki. Dangane da ziyarar, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zheng Zeguang, ya gaya wa manema labaru a yau Alhamis cewa, shugabannin 2 sun yi musayar ra'ayi kan wasu manyan batutuwa na kasa da kasa, inda suka cimma ra'ayi daya.

Shugabannin 2 sun ce kyautata huldar dake tsakanin Sin da Amurka ya dace da moriyar kasashen 2, wanda kuma hakan zai biya bukatun gamayyar kasa da kasa. Sa'an nan sun yarda da kara nuna goyon baya ga MDD kan aikinta na tabbatar da zaman lafiya, gami da taimakawa wasu kasashen dake nahiyar Afirka a wannan fanni.(Bello Wang)