logo

HAUSA

Kwararre: Takaddamar cinikayya dake tsakanin Sin Amurka na iya shafar harkokin kasuwancin Amurka

2017-08-29 11:35:49 CRI

Wani masani kan harkokin kasar Sin dake jami'ar Yale ta kasar Amurka Stephen Roach, ya bayyana cikin wani sharhi da ya rubuta cewa, matakai marasa dacewa da shugaba Trump na Amurka ya dauka game da kasar Sin, suna da matukar illa ga harkokin kasuwancin kasar ta Amurka har da kwastomomi.

A kwanakin baya ne dai wakilin cinikayya na kasar Amurka Robert Lighthizer ya gudanar da wani bincike kan ayyukan mallakar fasahar kasar Sin, karkashin doka ta 301 ta dokokin cinikayyar kasar Amurka ta shekarar 1974.

Rahotanni na nuna cewa, dokar wadda aka taba amfani da ita yadda ya kamata a shekarun 1980 da kuma farkon shekarun 1990 , ta baiwa shugaba Trump damar kakaba haraji ko wasu takunkuman da suka shafi harkokin cinikayya a kan kayayyakin da aka shigo da su daga kasar Sin. (Ibrahim)