logo

HAUSA

Ma'aikan jinya da suka zo daga kasar Sin wadanda ke tsayawa kan gaba na aikin kula da masu kamu da ciwo na kasar Namibia

2021-05-21 19:56:34 cri

A kasar Namibia da har yanzu ke samun yaduwar annobar numfashi ta COVID-19, ma'aikatan jinya daga kasar Sin suna kan gaba wajen ba da jinya. Ko da yake a ko wace rana suna sanye da rigar kariya ta likitanci wadda nauyinta yake sa su gumi mai yawa, kuma suna yin magana da babbar murya tare da marasa lafiya, hakan ya sa wuyansu yin ciwo, amma duk da haka sun zabi tsayawa a bakin aikinsu domin saukaka ciwon da mazauna yankin suka kamu da su, da kuma taimakawa Sinawa dake kasar wajen yaki da annobar.

Da karfe 7 da rabi na safe agogon wurin, mambobi hudu na kungiyar ba da jinya karo na 13 ta kasar Sin da ke ba da taimako ga kasar Namibia sun sanya tufafin kariya na likitanci kuma sun tashi zuwa aiki a Cibiyar ba da jinya ta hanyar amfani da alluran gargajiyar kasar Sin da ke asibitin Katutula wanda ba shi da nisa da masaukinsu. Suna kashe kwayoyin cuta ga wurin binciken masu kamuwa da cututtuka, kuma suna duba kayayyakin asibiti, bayan haka kuma sai su soma karbar marasa lafiya a wurin, a wannan lokacin kuma tuni akwai dogayen layuka a wajen wurin binciken. Ma’aikaciyar jinya ta kungiyar madam Liao Yun ta bayyana cewa,

"Adadin marasa lafiya da muke karba a kowace rana ya kai 60 zuwa 70. Ko da yake mun rage tsawon lokacin aiki sakamakon matakan rigakafi da shawo kan annobar COVID-19, amma hakan ba zai iya biyan bukatun marasa lafiya ba wajen samun jinya. Saboda marasa lafiya na da yawa, mu kan tsawaita lokacin aiki daga tashi daga aiki a karfe 11 da rabi zuwa karfe 1 ko 2 na rana. Ko da yake duk lokacin da muka sanya rigar kariya, mu kan yi zufa har gashi da tufafinmu kan jike zuwa lokacin da muka tashi daga aiki, amma don tabbatar da cewa babu matsala, dole ne mu tsaya kan aiki.”

Ma'aikan jinya da suka zo daga kasar Sin wadanda ke tsayawa kan gaba na aikin kula da masu kamu da ciwo na kasar Namibia_fororder_namibiya1.JPG

Kungiyar ba da jinya ta kasar Sin dake tallafawa kasar Namibia ta ko wane karo, ta hada da likitocin gargajiya na kasar Sin guda biyu da kuma ma'aikatan jinya guda biyu, kuma hukumar kula da lafiya ta lardin Zhejiang na kasar Sin ce ta tura kungiyar. Tun daga shekarar 1996 kuma, suna ta gudanar da aikin jinya a asibitin Katutula da ke Windhoek, babban birnin kasar.

Fasahar amfani da alluran gargajiyar kasar Sin ta yi suna sosai a kasar ta Namibia. Mutanen Namibiya da yawa da ke fama da cututtuka iri daban-daban kamar su ciwon kafafu da na kugu sun samu sauki bayan samun jinya ta hanyar amfani da wannan fasahar gargajiyar kasar Sin, haka kuma yanayin rayuwarsu ta samu kyautatuwa sosai. Saboda yabon da ta samu tsakanin marasa lafiya, cibiyar ba da jinya ta hanyar amfani da alluran gargajiyar kasar Sin kan karbi marasa lafiya da yawa, duk da cewa ana cikin wannan yanayin na musamman na yaki da annobar COVID-19. Godiya mai sahihanci da marasa lafiya suka yi, da kuma farin cikin da suke ji, sun burge ma’aikaciyar jinya Liao Yun, sun kuma sanya ta kawar da dukkan matsalolin da ta samu a yanayin tinkarar annobar, da kuma tsayawa kan ayyukanta.

“Wata mace mai matsakaicin shekaru wadda ke fama da ciwon kugu sosai na tsawon shekaru 10. A wancan lokacin, ta zo cibiyarmu na bincike bisa ra’ayin yin gwaji. An yi jinyarta ta hanyar amfani da allurar gargajiyar kasar Sin har sau 5, sai ciwon nata ya sami sauki sosai. Akwai kuma wani mai gadi, wanda ya sha fama da cutar shanyewar barin jiki na tsawon shekaru. Ya kan zo asibitin don samun jinyar alluran gargajiyar Sin karkashin taimakon ‘yan uwansa da ke tura keken guragu. Amma wata rana, sai muka gano cewa, a bisa rakiyar ‘yan uwansa, wannan mara lafiya ya iya takowa da kafarsa zuwa asibiti, kuma ba ya bukatar keken guragu, sun yi mamaki kuma sun yaba mana sosai. Yanzu, cibiyarmu na kara samun amincewa daga wajen masu kamu da ciwo. Kungiyar ba da jinyarmu ma ta kafa wata kyakkyawar shaida a kasar Namibia, a ra’ayin mazauna wurin kuma, ‘yan kungiyarmu sun kasance ‘likitoci masu kwarewa sosai’, su kan ce, ‘likitocin kasar Sin ne suka ba mu jinya har muka sami sauki, mun amince da likitoin kasar Sin.’ ”

Ma'aikan jinya da suka zo daga kasar Sin wadanda ke tsayawa kan gaba na aikin kula da masu kamu da ciwo na kasar Namibia_fororder_纳米比亚2.JPG

Game da madam Xu Yunmei, wacce ta kasance mai aikin jinya na tsawon shekaru 30, gogewarta game da ba da tallafin jinya a Afirka ita ce babbar darajar ruhin aikinta na jinya. Nuna kauna da hakuri da kuma kulawa sosai ga marasa lafiya, wannan ne ka’idar da take bi kan aikinta, tana kuma gudanar da aiki a kasar Namibia ne bisa ka’idar.

“Na fara aiki a matsayin mai aikin jinya a shekarar 1991. A gania na, idan an yi fatan samu warkewa daga ciwo, jinya na ba da amfani na kashi 3 cikin kashi 10, kulawa ma na kai wa kashi 7 cikin 10, don haka, yana da muhimmanci kwarai mu masu aikin jinya mu nuna kauna da hakuri a tsanake da kuma sauke nauyin aikinmu. Ban da wannan kuma, muna bukatar son ayyukanmu sosai, don kara kwarewarmu. A da na kasance ungozoma, wanda a cewar diyata, aiki ne mai faranta rai. Ina fuskantar jarirai sabon haihuwa a ko wace rana. Ba da tallafin jinya a Afirka wani nau'in aikin jinya ne na daban. Na koyi abubuwa masu yawa a nan, wadanda suke kasancewa arzikin ruhina.”

Baya ga aiki, Xu Yunmei ta kuma koyar da al’adun gargajiya na kasar Sin kamar su wasan kongfu na Taijiquan da Baduanjin ga abokan aikinta a asibitin ‘yan kasar Namibya. Ta ce, wannan ma wata hanya ce ta taimakawa likitoci da ma'aikatan jinya na wurin tinkarar matsaloli tare.

A sa’i daya kuma, Xu Yunmei ita ma ta koyi yaren mutanen wurin, kamar su “barka dai”, “na gode” da dai makamantan su, irin jimloli masu sauki sun kusanci dangantakar dake tsakaninta da mazaunan wurin, ta yadda 'yan Namibiya su ma suke jin annashuwa da kauna daga wajen ma'aikatan jinya na kasar Sin.

Baya ga ba da jinya ga mazauna wurin, kungiyar likitocin kasar Sin tana kuma da alhakin samar da shawarwarin kiwon lafiya ga Sinawan dake Namibia, da magance matsalolin gaggawa, da taimakawa Sinawa wajen yaki da annobar COVID-19 a kasar Namibia dake fama da annobar. kasancewar ma'aikatan kungiyar ta ba da tabbaci ga Sinawa dake kasar ta Namibia.