logo

HAUSA

Kasashen Afirka sun alkawarta karfafa tsarin kiwon lafiyar mata da kananan yara yayin da ake farfadowa daga annoba

2021-05-19 10:02:45 cri

Wakilan gwamnatocin kasashen Afirka, sun alkawarta aiwatar da matakan inganta tsarin kiwon lafiyar mata, da matasa, da kananan yara, yayin da ake farfadowa daga annobar COVID-19.

Da suke tsokaci yayin wani taron masu ruwa da tsaki ta yanar gizo, wakilan gwamnatoci daga Najeriya, Malawi, da Afirka ta kudu, da Liberia da Kenya, sun bayyana kula da lafiyar mata masu juna biyu, da jarirai, da matasa, a matsayin muhimmin aiki dake gaban gwamnatoci, duk kuwa da tsaikon aiwatar da shi da aka samu sakamakon barkewar annobar.

Taron wanda hukumomi masu tallafawa ayyukan kula da lafiyar al’umma na kasa da kasa suka shirya, ciki har da kawancen kungiyoyin tallafawa mata masu juna 2, da cibiyar tallafawa jarirai da lafiyar yara, da CORE Group, da Gavi, tare da cibiyar samar da kudade don tallafawa mata, da yara kanana da matasa, ya jaddada bukatar zuba jarin musamman, da kyautata manufofi, da inganta aiwatar da matakan gwamnati, tare da yayata manufofi a matakan farko na al’umma, ta yadda kan jama’a zai waye game da muhimmancin kula da lafiyar mata masu juna biyu, da jarirai yayin da ake fama da annoba.

Da yake tsokaci yayin taron, ministan lafiya na tarayyar Najeriya Osagie Ehanire, ya ce samar da isassun kudade, da amfani da sabbin kirkire kirkire, su ne muhimman matakai na inganta kula da lafiyar mata masu juna biyu, da jarirai da matasan nahiyar Afirka, musamman a gabar da nahiyar ke farfadowa daga gunguncewar tattalin arziki, mai nasaba da bullar annobar COVID-19.

Ehanire ya kara da cewa, Najeriya ta dora muhimmanci kan samar da kudade a muhimman sassa, kamar na samarwa al’umma magungunan ba da tazarar haihuwa masu inganci, dake taikamawa wajen kaucewa gamuwa da matsaloli masu nasaba da haihuwar da ba a shiryawa ba, ko zubar da ciki.  

Shi kuwa Zweli Lawrence Mkhize, ministan ma’aikatar lafiyar Afirka ta kudu, cewa ya yi kasar sa za ta yi bitar matakan yaki da annobar COVID-19, tare da cusa dabarun tabbatar da cewa, mata da matasa na samun kulawar lafiya, musamman a fannonin magungunar tazarar iyali da haihuwa lafiya.  (Saminu)