logo

HAUSA

Kasar Sin tana fatan Amurka za ta cika alkawarinta na raba alluran riga kafin COVID-19

2021-05-18 19:45:32 CRI

Kasar Sin tana maraba da Amurka ta cika alkawarin da ta yi, wajen raba alluran riga kafin COVID-19 da sauran kasashen duniya.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zho Lijian ne, ya bayyana haka Talatar nan, lokacin da yake kalubalantar matakin Amurka, game da kalamanta dangane da yadda kasar Sin take bayar da gudummawar riga kafin.

Shugaba Joe Biden na Amurka, ya bayyana cewa, kasarsa za ta raba alluran riga COVID-19 miliyan 80 da sauran kasashe, kuma adadin ya dara wanda kasashen Rasha da Sin suka bayar.

Zhao ya ce, riga kafi su ne ginshikin ceton rayuka, bai kuma bai kamata ba a yi amfani da su wajen samar da wani gibi na riga kafi ko cimma wata manufa ta siyasa.

Ya kara da cewa, kasar Sin ba za ta amfani da alluran riga kafi, wajen neman jagorantar duniya ko neman wata moriya daga sauran kasashe ba.(Ibrahim)

Ibrahim