logo

HAUSA

Wang Yi ya Tattauna da Majalisar Kula da Dangantakar Kasashen Wajen Amurka

2021-04-24 16:51:09 cri

Wang Yi ya Tattauna da Majalisar Kula da Dangantakar Kasashen Wajen Amurka_fororder_b03533fa828ba61e0d3d24e08ed5f302324e591c

Wakilin majalisar gudanarwa kuma Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Wang Yi, ya tattauna jiya Jumma’a, da Majalisar Kula Da Alakar kasashen waje na Amurka ta kafar bidiyo. Shugaban majalisar, Richard Nathan Haass ne ya dauki nauyin shirya taron, wanda ya samu mahalarta kusan 500 daga bangarori daban daban na Amurka.

Wang Yi ya bayyana ra’ayoyinsa biyar kan yadda za’a kalli alakar dake tsakanin Sin da Amurka bisa hangen nesa: Da farko, yana fatan Amurka za ta yi duba da fahimta kan ci gaban kasar Sin yadda ya kamata. Na biyu, yana fatan Amurka da Sin za su hau kan wata sabuwar hanyar zaman lafiya tare da hadin kai irin na samun nasara tare. Na uku, yana fatan Amurka za ta mutunta tare da amincewa da hanyoyi da tsare-tsare da kasar Sin ta zabarwa kanta. Na hudu, yana fatan Amurka za ta aiwatar da ainihin ra’ayin kasancewar bangarori da dama. Na biyar, yana fatan Amurka za ta daina tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin.

Baya ga haka kuma, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin na tsayawa kan bin hanyar neman ci gaba cikin lumana, wadda za ta bambanta da hanyar gargajiya da manyan kasashen suke bi. Ya ce nasarar da bangare daya daga cikin kasashen biyu ya cimma, ba ya nufin faduwar dayar bangaren. Yana mai cewa duniya zata fi son ganin kasashen Sin da Amurka mafi nagarta. (Bilkisu Xin)