logo

HAUSA

Afrika ta kudu zata ware karin albarkatun yaki da cutar HIV/AIDS

2020-12-02 10:24:03 CRI

Mataimakin shugaban kasar Afrika ta kudu David Mabuza, ya ce dukkan asibitocin gwamnatin kasar sun shirya tsaf wajen sadaukar da karin albarkatu domin yaki da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDS, da tarin TB, da annobar COVID-19.

Mabuza, wanda shi ne ke jagorantar kwamitin yaki da cutar AIDS na kasar, ya bayyana a jawabin da ya gabatar a lokacin bikin tunawa da ranar yaki da cutar AIDS ta duniya na wannan shekarar wanda aka gudanar a cibiyar kiwon lafiya ta Itireleng dake yankin Dobsonville, Soweto.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, tasirin annobar COVID-19 ya haifar da mummunar illa ga shirin yaki da cutar AIDS a kasar.

Game da batun yaki da cutar mai karya garkuwar jiki, mataimakin shugaban kasar yace, kasarsa ta samu manyan nasarori a shekaru goma da suka shude wajen dakile sabbin masu kamuwa da cutar.

Ya ce a halin yanzu za a mayar da hankali wajen fadada shirin kula da lafiyar masu fama da cutar kuma za a fi bayar da fifiko kan mutane marasa galihu da suka hada da mata.

A cewarsa mutane marasa galihu za a baiwa fifiko, musamman wadanda suka fi fuskantar barazanar hadarin kamuwa da cutar, kamar mata matasa, da kananan yara mata, da karuwai, da makamantansu.

Akwai sama da mutane miliyan 7 dake dauke da kwayar cutar HIV a Afrika ta kudu kuma sama da miliyan 4 suna kan tsarin maganin cutar, a cewar Mabuza, ya kara da cewa, ana shirin kara yawan mutanen da aka dora su kan tsarin maganin cutar.(Ahmad)