logo

HAUSA

Ya kamata a kara mai da hankali kan wadanda suke dauke da cutar Aids a yayin da ake tinkarar COCID-19

2020-12-01 20:05:00 CRI

Ya kamata a kara mai da hankali kan wadanda suke dauke da cutar Aids a yayin da ake tinkarar COCID-19

Ranar 1 ga watan Disamban kowacce shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware da nufin wayar da kai kan yaki da cutar kanjamau mai karya garkuwar jiki. A kan gudanar da shirye-shirye a fadin duniya a wannan rana, da nufin kara wayar da kai da kula da masu cutar da kuma tunawa da wadanda suka rasa rayuka sanadiyyarta.

A bana, hankalin duniya ya karkata kan annobar COVID-19 da kuma yadda annoba ke mummunan tasiri kan rayuka da zaman takewa. Wannan kuma na kara nuna yadda lafiya ke hade da sauran muhimman batutuwa. Bisa la’akari da hakan ne aka yi wa ranar a bana taken, “Hadin gwiwa da daukar nauyi tare a duniya”. Sabo da haka, ya kamata a kara mai da hankali kan wadanda suke dauke da cutar Aids a yayin da ake tinkarar COCID-19.

COVID-19 ya nunawa duniya cewa, yayin da annoba ta barke, babu wanda zai tsira har sai kowa ya tsira. Dole ne idan ana son samun nasara, a tafi tare. Kawar da kyama da tsangwama, da mayar da hankali kan mutane da tabbatar da kare hakkokinsu da daukar matakan tunkarar wariyar jinsi na da muhimmanci wajen kawo karshen cututtukan kanjamau da COVID-19.

Ya kamata a kara mai da hankali kan wadanda suke dauke da cutar Aids a yayin da ake tinkarar COCID-19

Cikin wani sabon rahotonsa mai taken shawo kan annoba ta hanyar sanya mutane a matsayin jigo, shirin yaki da cutar kanjamau na MDD UNAIDS, ya yi kira ga kasashen duniya su kara zuba kudi a fannin tunkarar annoba tare da daukar sabbin dabarun da burikan da za su haifar da kyakkyawan sakamako wajen kawo karshen cutar Kanjamau. Idan aka cimma wadannan burika, to ba makawa duniya za ta koma kan tafarkin kawo karshen cutar a matsayin barzana ga lafiyar al’umma, zuwa shekarar 2030.

Alkaluma sun nuna cewa, mutane miliyan 38 ne ke dauke da cutar a duniya, kana sabbin mutane miliyan 1.7 ne suka kamu da ita, sai kuma 690,000 da suka mutu sanadiyyarta cikin shekara guda da ta gabata.

Tun ma kafin barkewar annobar COVID-19, rahotanni sun nuna cewa kuduri da karkashin yaki da cutar sun ragu a duniya, sannan barkewar cutar da kuma yadda take saurin yaduwa, sun kara haifar da koma baya ta fuskar yaki da Kanjamau. Bisa la’akari da tasirin annobar COVID-19 kan yaki da kanjamau, an yi kiyasin samun karin mutane 123,000 zuwa 293,000 da za su kamu da cutar, sai kuma karin mutane 69,000 zuwa 148,000 da za ta yi ajalinsu tsakanin shekarar 2020 zuwa 2022.

Don haka, ya kamata annobar COVID-19 ta kara zaburar da wannan aiki. Haka zalika, wayar da kan al’umma na da mutukar muhimmanci wajen kawo karshen cutar. Akwai bukatar mutane su san matsayinsu dangane da cutar, sannan su fahimci yadda za su kare kansu da kuma yadda za su rika mu’amala da wadanda suke dauke da ita, wanda zai taka rawa gaya wajen ganin bayanta. (Faeza Mustapha)