logo

HAUSA

An Tono Munafuncin ‘Yan Siyasar Kasashen Yammacin Duniya Kan Hakkin Dan Adam Na Xinjiang

2021-04-30 21:33:01 CRI

An Tono Munafuncin ‘Yan Siyasar Kasashen Yammacin Duniya Kan Hakkin Dan Adam Na Xinjiang_fororder_xj

A yayin taron manema labaru da aka gudanar, dangane da batun jihar Xinjiang ta kasar Sin yau Jumma’a a nan birnin Beijing, Ailida Tuerahemaitifa, wadda ke aiki a wani kamfanin samar da tufafi na yankin Yili da ke jihar Xinjiang, ta yi tambayar cewa, “muna aiki a kamfaninmu ne bisa radin kanmu. Ba a nuna mana bambanci bisa addini, salon zaman rayuwa, yaren kabilarmu a kamfaninmu. Me ya sa wasu ke cewa, ana tilasta mana yin aiki?”

Gabanin ranar kwadago ta duniya a ranar 1 ga watan Mayun bana, wasu ‘yan kwadago daga jihar Xinjiang sun yi karin bayani, game da yadda suka ji dadin zaman rayuwarsu, ta hanyar yin aiki tukuru, a yayin taron manema labaran. Labaransu sun sake shaida cewa, zarge-zargen wasu ‘yan kasashen yammacin duniya masu adawa da kasar Sin, cewa wai ana tilasta wa mutane aiki a Xinjiang, karya ce ke nan.

Tsokacin da aka yi, na wai ana tilasta wa mutane aiki a Xinjiang, karya ce da kasashen yammacin duniya suka sha yadawa a duniya, domin bata sunan Xinjiang. Wadanda suka kulla makarkashiya kan kasar Sin, sun kau da idanunsu daga yadda ake amfani da manyan injuna da yawa a Xinjiang. Sun yi amfani da rahoton nazari, masu cike da karya da Adrian Zenz, da sauran irinsa suka rubuta, wajen shafa wa Xinjiang kashin kaji, da sunan wai kiyaye hakkin dan Adam. Yunkurinsu shi ne gurgunta hadin gwiwa a tsakanin Xinjiang da sauran sassan duniya ta fuskar samar da kaya, da illata karfin kamfanonin kasar Sin na yin takara a duniya, da hana ci gaban kasar Sin bisa fakewa da Xinjiang.

Amma duk da karyar da wasu mutanen kasashen yammacin duniya masu adawa da kasar Sin suka sha yi, ba za a hana Xinjiang ta samu ci gaba da wadata ba, kana kuma ba za a hana al’ummar Xinjiang su kara jin dadin zaman rayuwarsu ba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan