logo

HAUSA

Kamata ya yi tsoffafi su motsa jiki domin kara karfinsu

2021-03-28 09:41:29 CRI

Kamata ya yi tsoffafi su motsa jiki domin kara karfinsu_fororder_src=http___5b0988e595225.cdn.sohucs.com_images_20190325_600aa870d9f84f3f9e9495f748517ffa.jpeg&refer=http___5b0988e595225.cdn.sohucs

Yanzu haka ga alama dukkan wadanda suka motsa jiki domin samun kwanji a dakin motsa jiki, matasa ne. Duk da tsoffafi suna motsa jiki kullum, amma ba safai su kan motsa jiki don kara karfinsu ba. Amma wani sabon nazari ya shaida mana cewa, idan tsoffafi sun motsa jiki ta hanyar da ta dace don kara karfinsu da samun kwanji, to, zai taimaka wajen lafiyarsu da kuma tsawaita tsawon rayuwarsu.

Hadaddiyar kungiyar kula da karfin jiki da yanayin jiki ta kasar Amurka wato NSCA a takaice ta ba da wata sanarwa a kwanan baya cewa, tsoffafi su kan fuskanci matsalar koma baya a tunani, jiki, da ingancin zaman rayuwa. Wani nazarin da aka gudanar bisa gudummowar kungiyar NSCA ya nuna cewa, motsa jiki ta hanyar da ta dace don kara karfinsu da samun kwanji, wata kyakkyawar hanya ce wajen dakatar da koma-bayan da muka ambata a baya.

Nazarin ya yi karin bayani cewa, idan tsoffafi sun rika motsa jiki don kara karfinsu da samun kwanji sau 2 zuwa 3 a ko wane mako, to, duk da suna fama da cututtukan da suka dade suna adabar su, karfinsu na zaman rayuwa zai samu kyautatuwa.

Ban da haka kuma, motsa jiki ta hanyar da ta dace don kara karfinsu da samun kwanji yana taimakawa wajen kyautata samun daidaito a jiki, tabbatar da ingancin kashi, kyautata tunani, tare da rage barazanar kamuwa da ciwon zuciya, amosanin gabbai, ciwon sukari da lalacewar kashi.

Nazarin ya kuma ambato cewa, a yawancin lokuta, motsa jiki ta hanyar da ta dace yana amfanawa lafiyar tsoffafi, gwargwadon barazanar da suke fuskanta. Amma duk da haka, masu nazarin sun dauki kasar Amurka a matsayin wani misali, inda suka nuna cewa, a cikin tsoffafin da shekarunsu suka wuce 75 da haihuwa, kaso 8.7 ne kawai daga cikinsu suke motsa jiki ta hanyar da ta dace don kara karfinsu da samun kwanji a lokacin hutu. Muhimman dalilan da sauran suka ambato dangane da yadda ba su motsa jiki su ne, rashin tsaro, jin tsoro, jin ciwo, jin gajiya, da rashin isasshen goyon baya ta fuskar zaman al’ummar kasa.

Kungiyar NSCA ta ba da shawara filla-filla ga tsoffafi da su motsa jiki don kara karfinsu da samun kwanji, a kokarin taimaka musu kyautata motsa jiki yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan