logo

HAUSA

Yin gudu na dogon zango yana taimakawa wajen rage hawan jini da hana toshewar hanyoyin jini

2021-04-13 07:47:25 CRI

Yin gudu na dogon zango yana taimakawa wajen rage hawan jini da hana toshewar hanyoyin jini_fororder_src=http___n5.cmsfile.pg0.cn_group1_M00_29_7F_Cgqg11aa57CAeN07AAFR9_k4o48746&refer=http___n5.cmsfile.pg0

Wani sabon nazari da jami’ar University College London ta kasar Birtaniya ta gudanar ya nuna cewa, idan an dauki tsawon lokaci ana samun horo ta fuskar yin gudu na dogon zango, tare da shiga gasar gudun dogon zango wato Marathon, to, hakan zai iya taimakawa wajen rage hawan jini da kuma hana toshewar hanyoyin jini.

Masu nazari daga jami’ar University College London sun gayyaci mutane 138 masu koshin lafiya, kana karo na farko da suka shiga gasar gudun dogon zango wato Marathon, don su shiga nazarinsu. Matsakaicin shekarun wadannan mutane ya kai shekaru 37 a duniya. Kana kaso 49 daga cikinsu maza ne. Kafin su shiga nazarin, tsawon lokacin da su kan dauka suna yin gudu a ko wane mako bai wuce sa’o’i 2 ba. Wadannan mutane sun dauki tsawon lokaci suna samun horo domin shiga gasar gudun yada kanin wani.

Masu nazarin sun rubuta bayanan lafiyar wadannan mutane kafin su samu horo da kuma bayan da suka kammala gasar gudun dogon zango, inda suka auna hawan jininsu da lafiyar hanyoyin jininsu bisa fasahar zamani. Matsalar toshewar hanyoyin jini tana kara barazanar kamuwa da ciwon bugun zuciya fiye da kima.

Masu nazarin sun gano cewa, bayan da wadannan mutane suka samu horo da kuma shiga gasar Marathon, hawan jininsu ya dan ragu, haka kuma yadda hanyoyin jininsu ke toshewa ya ragu. A sa’i daya kuma, masu gudun dogon zango wato Marathon tsoffafi da kuma masu gudu na yau da kullum sun fi cin gajiya, musamman ma maza.

An kaddamar da rahoton nazarin cikin mujallar kungiyar masana ilmin ciwon zuciya ta kasar Amurka.

Dangane da wannan rahoton nazari, madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, wannan sakamakon nazari ya nuna mana cewa, sauya salon zaman rayuwa yana taimakawa wajen rage barazanar kamuwa da cututtuka sakamakon tsufa, haka kuma idan mun duba sakamakon nazarin da aka gudanar kan tsoffafi da kuma mutane wadanda ba su yin gudu da sauri, to, za mu iya gane cewa, a ko da yaushe ba a makara wajen fara motsa jiki. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan