logo

HAUSA

Tekun Kudancin Kasar Sin Ba Dandali Ba Ne da Amurka za ta yi Danniya

2021-04-09 20:53:42 CRI

A ranar 7 ga wata, rukunin babban jirgin ruwa mai dauke da jiragen saman yaki na USS Theodore Roosevelt karkashin shugabancin mayakan ruwan Amurka sun kammala atisayen soja a tekun kudancin kasar Sin. Wannan ne karo na 3 da babban jirgin ruwa mai dauke da jiragen saman yaki na USS Theodore Roosevelt ya kutsa kai cikin tekun kudancin kasar Sin a bana, lamarin da ya sake shaida cewa, Amurka babbar barazana ce ga zaman lafiyar tekun kudancin kasar Sin.

Amma bisa yanayin da ake ciki yanzu, Amurka ba za ta cimma burinta na tada zaune tsaye a tekun kudancin kasar Sin ba.

Sakamakon kokarin da kasar Sin da kasashe mambobin kungiyar ASEAN suke yi cikin hadin gwiwa, ya sa an samu kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin. Bangarorin 2 suna inganta hadin kansu a batutuwan da suke shafar tekun da gaggauta yin tattaunawa kan ka’idojin ayyuka a tekun kudancin kasar Sin. Suna da imani, kwarewa da hazaka wajen daidaita sabani yadda ya kamata. Kwanan baya, shugaba Rodrigo Duterte na kasar Philippines ya bayyana fatansa a fili na daidaita takaddamar da ke tsakanin kasarsa da Sin kan yankunan kasa cikin ruwan sanyi. Kana, kwanan baya ministocin harkokin wajen kasashe 4 na kungiyar ASEAN sun ziyarci kasar Sin, lamarin da ya nuna cewa, kasashe masu ruwa da tsaki ba su son abubuwan da Amurka ta ke yi amfani na nuna danniya.

Tekun kudancin kasar Sin, ba wani dandali ba ne da Amurka za ta yi danniyar da ta saba. Yadda Amurka take yunkurin tada zaune tsaya, ba za ta bata aniya da kokarin kasashen da ke yankin na kara azama kan samun ci gaba cikin lumana. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan