logo

HAUSA

Sin ta bukaci Amurka da ta daina abubuwan da take game da tekun kudancin kasar Sin

2019-08-27 19:51:16 cri

Kasar Sin ta bukaci kasar Amurka, da ta daina munanan abubuwan da take yi, ta taka rawar da ta dace ta kuma ba da muhimmiyar gudummawa a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, shi ne ya bayyana hakan yau, a taron manema labarai da aka saba gudanarwa, yayin da yake mayar da martani kan zargin da ma'aikatar tsaron Amurka ta yi cewa, a baya-bayan nan kasar Sin ta sake tsoma baki a ayyukan hakar mai da iskar gas da Vietnam da dade tana yi a yankin tekun kudancin kasar Sin.

Ya ce, wannan batu ba boyayyen abu ba ne. Amurka tana ta furta kalaman da ba su dace ba kan wannan batu, inda take mayar da fari baki, don haka kasar Sin tana adawa da wannan mataki.

Geng ya ce, kasar Sin tana martaba dokokin kasa da kasa, kuma har kullum tana kare 'yanci da muradunta dake shiyyar bisa dokokin kasa da kasa, tana kuma kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar baki daya.(Ibrahim)