logo

HAUSA

Ana cigaba da yin bincike a tekun kudancin kasar Sin

2017-07-24 13:43:46 CRI

Mai gudanar da binciken jirgin ruwa Kexue ya bar tashar ruwan Xiamen dake gabashin kasar Sin a lardin Fujian a ranar Lahadi domin cigaba da tafiyar da yake yi don gudanar da aikin bincike a tekun kudancin kasar Sin.

Sun Song, kwararren masanin kimiyya dake aiki karkashin wannan shirin, ya bayyana cewa, a lokacin zagaye na biyu na wannan aiki, masana kimiyyar zasu gwada yadda mutun-mutumin da kasar Sin ta kafa a karkashin teku suke aiki tare da hadin gwiwar wasu nau'urorin zamani dake karkashin tekun.

A cewar Sun, na'urorin da aka kafa a karkashin tekun zasu gudanar da aikin tattaro dukkan abubuwan dake wakana a karkashin tekun da kuma gano duk wasu sinadarai da ake amfani dasu a tekun da daukar hoton abubuwan dake faruwa a cikin tekun.

Kexue ya bar Qingdao na gabashin kasar Sin dake lardin Shandong a ranar 10 ga watan Yuli domin gudanar da ayyukan kimiyya, kuma ya dan tsaya a Xiamen bayan kammala aikinsa zagaye na farko.

A matakin farko, kimanin na'urorin daukar hotunan 12 ne kasar Sin ta kafa a karkashin tekun domin gudanar da aikin binciken kimiyyar a tekun kudancin kasar Sin, kuma zasu dinga samar da bayanai. Wannan shine na'urori mafiya yawa da suke gudanar da ayyuka a lokaci guda a wannan yankin.