logo

HAUSA

Yin rayuwa ta hanyar da ta dace yana rage barazanar kamuwa da cutar karancin basira

2021-01-31 10:00:06 CRI

Yin rayuwa ta hanyar da ta dace yana rage barazanar kamuwa da cutar karancin basira_fororder_u=3191428973,3289211308&fm=26&gp=0

Wata tawagar nazari ta kasa da kasa ta gano a kwanan baya cewa, ko da yake kamuwa da cutar karancin basira yana da nasaba da batun gadon dabi'un halitta, amma yin rayuwa ta hanyar da ta dace yana rage barazanar kamuwa da cutar ta karancin basira sosai.

Wannan tawagar da ke karkashin shugabancin masu nasari daga jami’ar Exeter ta kasar Birtaniya ta kaddamar da rahoton nazari cikin mujallar hukumar ilmin likitanci ta kasar Amurka wato The Journal of the American Medical Association a Turance, inda suka nuna cewa, sun tantance bayanan da suka shafi Turawa fiye da dubu 196 ‘yan shekaru fiye da 60, sun kuma yi kidaya kan barazanar da suka fuskanta wajen gadon cutar ta karancin basira daga mahaifa, salon zaman rayuwarsu da barazanar da suka fuskanta a zahiri wajen kamuwa da cutar.

Masu nazarin sun tanadi rashin shan taba, motsa jiki kullum, cin abinci ta hanyar da ta dace, da shan giya kadan cikin kyakkyawan salon zaman rayuwar dan Adam.

Tantancewar ta nuna cewa, duk da barazanar da aka fuskanta wajen gadon cutar ta karancin basira daga mahaifa, zaman rayuwa ta hanyar da ta dace yana da nasaba da raguwar barazanar kamuwa da cutar karancin basira a zahiri. In an kwatanta su da mutane wadanda ba su fuskantar mummunar barazanar gadon cutar ta karancin basira daga mahaifa, suna kuma rayuwa ta hanyar da ta dace, mutanen dake fuskantar mummunar barazanar gadon cutar ta karancin basira daga mahaifa, kuma ba su rayu yadda ya kamata, sun fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar har sau uku.

A cikin mutane wadanda suke fuskantar babbar barazanar gadon cutar ta karancin basira daga mahaifa, idan wasu suna rayuwa ta hanyar da ta dace, to, barazanar da suke fuskanta wajen kamuwa da cutar ta ragu da kaso 32, in an kwatanta su da wadanda ba su rayuwa yadda ya kamata.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, wasu mutane suna ganin cewa, tabbas za su kamu da cutar karancin basira wata rana, saboda kamuwa da cutar yana da nasaba da kwayoyin dabi'ar halittar dan Adam. Amma sabon nazarin ya musunta irin wannan ra’ayi. Idan mutane suna rayuwa ta hanyar da ta dace, alal misali, ba su sha taba ba, su kan motsa jiki kullum, suna cin abinci ta hanyar da ta dace, to, za su rage barazanar da suke fuskanta wajen kamuwa da cutar, duk da cewa, sun gaji kwayoyin dabi’ar halitta daga mahaifansu. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan