Wasan Yoga ya taimaka wa mazauna kauye wajen kara karfin jiki da jin dadin rayuwarsu
2021-01-25 14:37:27 CRI
A da can baya, Yugouliang, wani kauye a gundumar Zhangbei na lardin Hebei dake arewacin kasar Sin, ya yi fama da talauci. Amma yanzu ya yi adabo da shi baki daya, inda kuma ake kiransa da kauyen da ya fara wasan motsa jiki na Yoga. Amma me ya sa ake kiransa da haka? A kullum, dukkan mazauna kauyen kan yi wasan Yoga, kafin da bayan aiki, domin kasancewa cikin koshin lafiya.
A kauyen Yugouliang, ba a samun amfani gona mai yawa, saboda matsalar yanayi a yankin Bashang na jihar Mongolia ta gida da ke kusa da shi. Galibin matasan yankin sun bar kauyen domin ci rani a manyan birane. Yanzu, yara da tsoffi ne yawanci ke zaune a kauyen.
A cewar babban sakataren kauyen, Lu Wenzhen, yanayin sanyi da rashin kyan yanayin rayuwa da ayyuka masu tsanani na haifar da matsalar lafiya da rashin ingancin rayuwa ga tsoffin dake kauyen.
Da yake bi gida-gida yana tattaunawa da mazauna kauyen, Lu ya gano cewa, salon zaman dukkan mazaunan kauyen iri guda ne, wato salon Pantui, wanda ke nufin zama kafa daya kan daya a kan gado. Bisa abun da ya gano, sai ya kirkiro dabarar taimaka musu kara karfin jikinsu ta hanyar Yoga. Lu ya yi imanin cewa, sai da karfin jiki mazauna kauyen za su tashi tsaye su fatattaki talauci.
Kusan kaso 60 daga cikin masu fama da talauci, rashin lafiya ne ya jefa su cikin yanayin. “idan aka yi amfani da Yoga wajen inganta lafiyar tsoffi, kudin da ake kashewa na zuwa asibiti zai ragu sosai,” cewar Lu.
Ya sayi tabarmar Yoga guda 100 ta intanet, ya kuma raba ga mazauna kauyen kyauta, domin karfafa musu gwiwar fara wasan Yoga. A wani lokaci, kusan mutane fiye da 60 ne ke yin Yoga a lokaci guda. Shirin ya ja hankalin manoma da ma’aikatan lafiya da malamai da shugabannin kauyukan dake kewaye da Yugouliang da ma shugabannin kungiyoyin mata na yankin.
Sha’awarsa da mutanen kauyuka makwafta suka yi, ya bada kwarin gwiwa sosai, da kuma muradin ci gaba da yinsa, lamarin da ya sabuntawa mutanen muhimmancin kyautata karfin jikinsu. Yin Yoga na karfafa jiki da taimakawa lafiyar kwakwalwa, lamarin dake saukaka matsin da yaransu ke fuskanta.
Labarin wasan motsa jiki na Yoga na Yugouliang, ya samu sahalewar hukumar kula da wasanni ta kasar Sin, kuma ya ja hankalin Sinawa da kafofin watsa labarai na kasa da kasa. Sabili da rahotannin kafafen yada labarai da dama, kauyen ya yi saurin yin fice.
“Yanzu mazaunan da kan taru su yi hira da wasanni a lokacin da ba su da aiki, suna wasan Yoga,” cewar Lu. Masoya Yoga, daga dukkan fadin kasar Sin kan yi tururuwa zuwa kauyen domin su ga salon Yoga na kauyen.
Rukunin aikin yaki da talauci na kauyen da kwamitin kauyen na aiki tare domin aiwatar da dadadden shirin raya yankin na samar da kayayyakin kiwon lafiya da inganta kayayyakin more rayuwa ciki har da tituna da kyautata muhalli da fitilun kan titi, wadanda suka sauya kammanin kauyen .
Lu ya kuma taimakawa mazauna kauyen yin rajistar tambarin cinikayya na “Yugouliang” kuma ya yi amfani da tambarin wajen tallata sabon nau’in dangin hatsi na Quinoa da aka shuka a kauyen. Quinoa na Yugouliang ya shahara bayan mutanen kauyen sun fadada hanyoyinsu na talla a intanet.
Wu Qilian, mai shekaru 77, mace ce mai kunya a kauyen Yuguoliang. A lokacin da mutane suka fara wasan Yoga, Wu kan tsaya a gefe tana kwaikwayo da hannu.
Ta ba sauran mutanen mamaki a lokacin da ta fara, musammam ma bayan ta fara yi sosai. Saboda yadda ta kware, Wu, wadda ba ta fita, ta samu damar yin tafiye-tafiye a fadin kasar Sin, don hira a cikin shirye-shiryen talabijin. Ta ma taba yin Yogar kai tsaye a dandali yayin bikin bazara a 2019, wanda aka watsa ta gidan tashar talabijin na lardin Hunan.
Xu Biao, jikan Wu, matashi ne dake aikin ci rani. Ya yi mamakin ganin kakarsa tana Yoga da ya je kauyen domin bikin bazara a 2019. Ya dauki gajerun bidiyon da ya wallafa kan shafin Kuaishou, wani dandalin wallafa bidiyo a intanet, inda mutane sama da 30,000 suka kalli bidiyo na farko da ya wallafa, yayin da na biyu ya samu masu kallo kimanin dubu 175.
Ya samu wata dama daga sha’awar da masu amfani da intanet suka nuna kan bidiyon, don haka ya rika wallafa bidiyon kakaninsa akai-akai. Shafinsa na Kuaishou ya ja hankalin mabiya kusan dubu 20, ya kuma samu masu sha’awa sama da miliyan 3, inda ya zama daya daga cikin shafunan wallafa bidiyo mafiya fice.
Xu ya kuma gwada harkar wallafa bidiyo kai tsaye. Da taimakon rukunin aikin yaki da talauci na kauyen, ya halarci wani kwas na horo a Shijiazhuang, babban birnin Hebei, domin koyon wallafa bidiyo kai tsaye da dabarun daukar bidiyo. Karkashin jagorancin kauyen, ya dauki bidiyon kwas din Yoga, wanda ya samar masa da sama da yuan 5,000, kwatankwacin dala 746 a wata na farko.
Jin Xiuying, shugabar kungiyar mata ta Yugouliang, daya ce daga cikin wadanda suka ci gajiyar kafofin sada zumunta irinsu Kuaishou. A matsayinta na mai wallafa bidiyo dake da mabiya sama da dubu 150, yanzu ta kware wajen daukar gajerun bidiyo, kuma tana sayar da amfanin gona kamar Quinoa ta dandalin wallafa bidiyo kai tsaye na intanet. Ta kan kuma dauki bidiyon azuzuwan koyar da Yoga, inda take samun yuan 6,000 a ko wane wata.
Kauyen na ci gaba da samun damarmakin ci gaba da bai samu ba a baya, wanda ke samo asali daga karuwar ingancin sufuri da kuma ci gaban da aka samu na hadewar Beijing da Tianjin da Hebei. Yanayin farin ciki da gamsuwa da kwarin gwiwar da mutanen kauyen ke da shi, zai burge wadanda suka ziyarci Yugouliang.