logo

HAUSA

Hare haren ‘yan bindiga sun hallaka a kalla mutane 137 a yankin Tahoua na Nijar

2021-03-23 09:45:42 CRI

Rahotanni na cewa, wasu hare haren ‘yan bindiga sun hallaka a kalla mutane 137 a yankin Tahoua na jamhuriyar Nijar. A ranar Lahadi ne dai wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ko su wa ye ba, suka kaddamar da hare haren kan mai uwa da wabi, a kauyukan Intazayene, da Bakorat da Wistane dake jihar Tahoua, na yammacin jamhuriyar Nijar mai iyaka da kasar Mali.

Gwamnatin Nijar ta fitar da wata sanarwa dake tabbatar da aukuwar lamarin, tana mai cewa, an tsaurara matakan tsaro da na bincike, domin zakulo wadanda suka aikata wannan ta’asa, don gaggauta gurfanar da su gaban kuliya.

Kaza lika gwamnatin ta ayyana zaman makoki na kwanaki 3, wanda za a fara tun daga Talatar nan, za kuma a sassauto tutar kasa zuwa rabin sanda a dukkanin sassan kasar domin nuna alhinin aukuwar wannan lamari.

A baya bayan nan yankin yammacin Nijar, na fama da hare haren ‘yan ta’adda dake farwa fararen hula da jami’an tsaro, duk kuwa da sansanin dakarun kasar Faransa masu yaki da ta’addanci dake jibge a wannan yanki.  (Saminu)

Saminu