logo

HAUSA

Antonio Guterres ya jinjinawa gudanar babban zabe a Nijar

2020-12-29 09:36:55 CRI

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya jinjinawa gwamnati da al’ummar janhuriyar Nijar, bisa nasarar gudanar da babban zaben shugaban kasa da na ‘yan majalissar dokokin kasar.

Cikin wata sanarwa da ofishin sa ya fitar, Mr. Guterres ya kuma yabawa hukumomin tsaron kasar, bisa kokarin su na samar da kyakkyawan yanayin tsaro yayin zaben.

Jami’in ya kuma yi kira ga dukkanin sassan masu ruwa da tsaki a harkar siyasar kasar, da dukkanin magoya baya, da su tallafawa manufar wanzar da zaman lafiya, tare da warware duk wani sabani daka iya bullowa ta hanyar tattaunawa, tare da bin matakan shari’a.

Babban magatakardar MDDr ya kuma jaddada goyon bayan majalissar ga al’umma da gwamnatin Nijar, a kokarin su na karfafa dimokaradiyya, da ci gaba mai dorewa a kasar.

A ranar Lahadin karshen mako ne dai, aka kada kuri’u a zaben shugaban kasa da ‘yan majalissar dokokin Nijar, a zaben da ake wa kallon irin sa na farko da kasar ta yammacin Afirka ta gudanar, wanda zai ba da damar mika mulki daga zababbiyar gwamnati zuwa wata, tun bayan samun ‘yancin kai, a gabar da kuma ake kara fuskantar barazanar masu ikirarin Jihadi a yankin. (Saminu)