logo

HAUSA

An kaddamar da ginin layin dogo tsakanin Najeriya da janhuriyar Nijar

2021-02-10 10:26:46 CRI

An kaddamar da ginin layin dogo tsakanin Najeriya da janhuriyar Nijar_fororder_20210210-layin dogo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kaddamar da ginin layin dogo da zai hade wasu sassan arewacin Najeriya da janhuriyar Nijar. An kaddamar da aikin ne, wanda zai hada jihar Kano dake arewa maso yammacin kasar da birnin Maradi na janhuriyar Nijar a jiya Talata, yayin bikin kafa harsashin ginin da shugaban Najeriyar ya jagoranta ta kafar bidiyo.

Aikin mai tsawon kilomita 284, zai lakume kudi har dalar Amurka biliyan 1.959, ya samu amincewar majalissar zartaswar Najerya tun a watan Satumbar bara, kuma kamfanin Mota-Engil Group na kasar Portugal ne zai gudanar da shi.

An tsara kammala aikin mai kunshe da tashohin jirgin kasa 15 ne cikin shekaru 3 masu zuwa, kuma ana sa ran zai taimakawa raya tattalin arzikin jihohin Kano, da Katsina, da Jigawa dake arewa maso yammacin Najeriya, da kuma Maradi dake janhuriyar Nijar.

Cikin wani sakon da ministan sufurin Najeriya Rotimi Amaechi ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar 11 ga watan Janairu, ya ce kamfanin da zai gudanar da aikin, ya kuma amince ya gina wata jami’ar koyar da sassan ilmomi daban daban a kudancin kasar, yayin da yake ginin layin dogon. (Saminu Hassan)