logo

HAUSA

Allurar rigakafin da Sin ta samar ta taimakawa kasashen duniya wajen yakar COVID-19

2021-02-22 16:01:50 CRI

Allurar rigakafin da Sin ta samar ta taimakawa kasashen duniya wajen yakar COVID-19_fororder_微信图片_20210222153835

A kwanakin baya-bayan nan, kasar Sin ta mika wa kasashen duniya da dama allurar rigakafin cutar COVID-19 da ta samar, ciki hadda Zimbabwe da Senegal da Hungary da Peru da dai sauransu. Allurar ta taimakawa wadannan kasashe wajen yakar cutar da ta ke ci gaba da addabar duniya, har an ce ta zama tamkar wata kyauta da Sin ta samarwa duniya a yayin al’ummar Sinawa suka shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyarsu.

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya ce, ko da yake Sin ita kanta na matukar bukatar allurar, amma ta samarwa sauran kasashe ciki hadda kasarsa, inda ya bayyana gudunmawar da Sin take bayarwa a fannin yakar cutar a matsayin wadda ba za a iya mantawa ba.

A hakika dai, a watan Mayun shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi alkawarin cewa, Sin za ta mayar da allurar rigakafi a matsayin kaya ga kowa bayan ta cimma nasarar samar da ita, ta yadda kasashe masu tasowa za su samu damar samun rigakafin. Ga shi yanzu Sin tana kokarin cika alkawarinta.

Ya zuwa yanzu, Sin ta samar da gudummawar allurar ga kasashe masu tasowa 53 da suka gabatar da bukatunsu, kuma ta fitarwa kasashe 22 allurar. Baya ga haka, bisa bukatun WHO, Sin ta yanke shawarar samarwa shirin samar da allurar rigakafin cutar Covid-19 ta kasa da kasa wato COVAX, alluran da yawansu ya kai miliyan 10, don biyan bukatun kasashe masu tasowa. (Amina Xu)