logo

HAUSA

An yiwa shugabannin kasashe 8 allurar rigakafin cutar COVID-19 ta kasar Sin

2021-02-20 16:31:15 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce an yi wa a kalla shugabanni ko kusoshin gwamnatocin kasashe 8 allurar riga kafin COVID-19 da Sin ta samar, lamarin da ke shaida ingancin allurar.

Jaridar Washington Post ta ruwaito cewa, allurar ta kasar Sin, ta samarwa kasashe masu tasowa damar zabar irin allurar da ta dace. Dangane da haka, Hua Chunying, ta bayyanawa manema labarai a jiya cewa, burin hadin kan Sin da kasahen duniya shi ne, samarwa dukkanin kasashe allurar. A cewarta, kamata ya yi a rarraba allurar bisa adalci ba tare da nuna bambanci ba, ta yadda za a raba ta yadda ya kamata, musamman ma ga kasashe masu tasowa.

Daga cikin shugabannin kasashen da aka yi wa allurar ta kasar Sin, akwai na Turkiyya da Seychelles da Jordan da Indonesiya da Peru da Chile.  (Amina Xu)