logo

HAUSA

Kafar watsa labaran Kenya: Sin na daukar hakikanin matakan raba allurar rigakafin COVID-19 bisa adalci

2021-02-21 17:36:18 CRI

Kafar watsa labaran Kenya: Sin na daukar hakikanin matakan raba allurar rigakafin COVID-19 bisa adalci_fororder_1219-2

A ranar 19 ga wata, agogon kasar Kenya, jaridar The People ta kasar ta wallafa wani rahoto, inda aka yaba wa kasar Sin bisa cika alkawarin da ta yi, tana daukar hakikanin matakai domin rarraba allurar rigakafin cutar COVID-19 bisa adalci a fadin duniya.

A cikin rahoton, an yi nuni da cewa, annobar COVID-19 ta haifar da rikici a fadin duniya, yanzu haka yawon shakatawa tsakanin kasa da kasa ya katse, tattalin arzikin duniya ya koma baya, siyasar nuna fin karfi da tunanin yakin cacar baka sun sake kunnowa, kuma ra’ayin bangaranci da ba da kariya su ma suna sake bazuwa, ana iya cewa, bil Adama suna fuskantar hadari da kalubaloli da ba su taba ganin irinsu ba a baya, kana wasu kasashe suna siyasantar da annobar, suna adawa da dabarun kimiyya, har suna tattara allurar rigakafin cutar ta hanyar yin amfani da karfin siyasa, tare kuma da yin watsi da bukatun kasashen da suke fama da koma bayan tattalin arziki, alkaluman MDD ya nuna cewa, kasashen duniya 10 sun mallaki alluran rigakafin cutar COVID-19 kaso 75 bisa 100 na yawan alluran rigakafin a fadin duniya.

Rahoton ya jaddada cewa, ya dace sassa daban daban su hada kai domin yaki da nuna fifiko kan al’ummun kasashe daban daban, yayin da ake raba allurar rigakafin annobar, ta yadda za a raba allurar bisa adalci, musamman ma a kasashen dake fama da rikici.

A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin ta riga ta samar da tallafin allurar rigakafin ga kasashe masu tasowa da yawansu ya kai 53, kuma ta fitar da allurar ga kasashe 22, kana ta samar da allurar biliyan 1 ga shirin COVAX domin biyan bukatun kasashe masu tasowa.(Jamila)