logo

HAUSA

Kasar Sin ta shiryawa zurfafa dangantakarta da Algeria

2020-10-12 10:45:11 cri

Kasar Sin ta bayyana shirinta na kara inganta huldarta da Algeria a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da kimiyya, da fasaha, da yaki da ta'addanci, da nufin daukaka dangantakarsu.

Yang Jiechi, mamban ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar JKS ne ya bayyana haka, lokacin da yake ganawa da shugaban Algeria Abdelmajid Tebboune, a Algiers, babban birnin kasar dake arewacin Afrika.

A cewarsa, a shirye Sin take ta hada hannu da Algeria wajen hada shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ta kasar, da sabon tsarin farfado da tattalin arziki na Algeria, yayin da kuma suke ci gaba da karfafa abota da aminci a tsakaninsu.

A nasa bangaren, Shugaba Tebboune ya jinjinawa daddadiyar abotar dake tsakanin kasashen biyu da kuma taimako da amincinsu ga juna, yana mai kuma yabawa irin ci gaban da Sin ta samu.

Ya ce Algeria na daukar Shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da muhimmanci, kuma za ta hada hannu da Sin din wajen ingiza manyan ayyukan hadin gwiwa domin ba al'ummomin kasashen biyu damar kara cin gajiya dangantakar dake tsakaninsu.

Bugu da kari, shugaban na Algeria ya yabawa muhimmiyar rawar da Sin take takawa a harkokin da suka shafi duniya da kuma kokarin yaki da annobar COVID-19. (Fa'iza Mustapha)