logo

HAUSA

Gani Ya Kori Ji Dangane Da Batun Xinjiang

2021-02-04 19:59:53 CRI

Gani Ya Kori Ji Dangane Da Batun Xinjiang_fororder_xinjiang

A yammacin ranar 3 ga wata, a yayin wani taron da kasar Sin ta shirya ta kafar bidiyo tsakanin jakadun kasashen waje a Geneva da hukumomin MDD, jakadu fiye da 60 a wasu kasashen da ke Geneva, da wasu manyan jami’an MDD sun waiwayi ziyararsu a jihar Xinjiang ta kasar Sin a shekarun baya, sun kuma amince da kokarin da gwamnatin Sin ta yi wajen kara azama, kan raya kasa mai dorewa, da kuma kiyaye hakkin dan Adam. Gani ya kori ji. Abubuwan da wadannan jakadu suka gane wa idanunsu sun sake nuna cewa, jihar Xinjiang ta kasar Sin, wuri ne mai ni’ima.

Sa’an nan kuma kasar Sin ta fitar da wani rahoton kare hakkokin jama’a a bangaren masakun jihar ta Xinjiang, wanda ya jawo hankali sosai a gida da wajen kasar Sin. A matsayin sana’ar da ta fi samun yawan ma’aikatar a jihar Xinjiang, sana’ar masaka tana daya daga cikin muhimman hanyoyin da ake bi a jihar ta Xinjiang wajen fitar da mutane daga talauci a shekarun baya. Baya ga haka kuma, mazauna jihar Xinjiang sun samu damar yin aiki a sauran wuraren kasar. Don haka a watan Nuwamban shekarar 2020, karo na farko, an fitar da dukkan al’ummun jihar daga kangin talauci a tarihi.

Yadda mazauna jihar Xinjiang ’yan kananan kabilu suke rika kara kyautata zaman rayuwarsu ta hanyar yin aiki yadda ya kamata, ya musunta karya ta rashin kunya da wasu ’yan siyasar kasashen yammacin duniya suke yi game da jihar. (Tasallah Yuan)

 

 

 

 

 

 

Tasallah Yuan