logo

HAUSA

An gudanar da taron tallata Xinjiang a Geneva

2021-02-04 10:11:48 CRI

A jiya Laraba, zaunanniyar tawagar wakilan kasar Sin a Geneva tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur ta kasar Sin, suka gudanar da taron tallata jihar, inda jami’an diplomasiyya daga kasashe sama da 50 da jami’an ofishin babban kwamishinan kula da harkokin hakkin bil Adam ta MDD da masanan kwamitin kula da harkokin hakkil Bil Adam ta MDD dake Geneva, suka kara fahimtar kyakkyawan yanayin da jihar take ciki ta fannonin kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arziki da ingantacciyar rayuwar al’umma.

A jawabin da ya gabatar, zaunannen wakilin kasar Sin a Geneva, Mr.Chen Xu ya bayyana cewa, wasu kasashe da tsirarrun mutane ba sa son ganin irin yanayi mai kyau da ake ciki a jihar Xinjiang, don haka, suke ta kokarin mayar da fari baki da shafa wa kasar Sin bakin fenti.

Baya ga haka, wasu kasashe suna neman sanya matakan takunkumi, a yunkurin hana al’ummar jihar samun damar jin dadin rayuwarsu, matakin da ya samu rashin amincewa daga al’ummar jihar daga bangarori daban daban.

A jawaban da suka gabatar, jakadun kasashen Koriya ta Arewa da Rasha da Zimbabwe da Eritrea sun bayyana cewa, ta wannan taron, sun jin ta bakin mutane daga bangarori daban daban, kuma ci gaban jihar Xinjiang da ingantacciyar rayuwar al’ummar wurin sun burge su matuka, matakin da ya taimaka wa jami’an diplomasiyya da ke Geneva kara fahimtar hakikanin halin da ake ciki a jihar.(Lubabatu)