logo

HAUSA

Kofi yana sa hanji kara yin aiki amma ba ruwan lamarin da sinadarin Caffeine

2021-02-02 15:43:33 CRI

Kofi yana sa hanji kara yin aiki amma ba ruwan lamarin da sinadarin Caffeine_fororder_u=1667161495,2216855696&fm=26&gp=0

Masu karatu, wasu daga cikinku suna sha’awar shan kofi, ko a’a? Watakila kun san cewa, kofi ya sa zuwa bayan gida. Wani sakamakon nazari da aka gudanar kan dabbobi a kasar Amurka ya nuna mana cewa, hakika dai shan kofi yana sa hanji kara yin aiki, tare da sauya rukunonin kananan halittu masu rai dake cikin hanji. Amma dukkansu ba su da nasaba da yawan sinadarin Caffeine. Ya zuwa yanzu ba a san yadda kofi yake sa hanji kara yin aiki ba tukuna.

Masu nazari daga sashen ilmin likitanci na jami’ar Texas ta kasar AMurka sun yi nazari kan beraye. Sakamakon nazarin ya nuna cewa, idan an sanya kashin berayen a cikin ruwan da ke da kofi a ciki, kuma yawan kofi da ke cikin ruwan ya kai kaso 1.5, to, kananan halittu masu rai da ke cikin kashin berayen ba za su girma yadda ya kamata ba. Idan an ajiye kashin berayen cikin ruwan da ke da kofi a ciki, kuma yawan kofi da ke cikin ruwan ya kai kaso 3, to, an kara rage yadda kananan halittu masu rai suke girma. Har ila yau kuma masu nazarin sun gano cewa, haka lamarin yake a cikin ruwan da ke da kofin da babu sinadarin Caffeine a ciki.

Daga bisani kuma, masu nazarin sun sanya beraye na tsawon kwanaki 3 a jere suna shan kofi, inda suka gano cewa, jimilar yawan kananan halittu masu rai da ke cikin hanjin berayen ta ragu. Duk da haka, masu nazarin sun yi nuni da cewa, akwai bukatar su ci gaba da nazarinsu don tabbatar da cewa, raguwar jimilar yawan kananan halittu masu rai a cikin hanjin berayen tana amfana wa lafiyar hanji ko a’a.

Ban da haka kuma, masu nazarin sun gano cewa, bayan da berayen suka dauki tsawon lokaci suna shan kofi, hakan ya kara karfin jijiyoyin da ke hanji da ma uwar hanjinsu.

Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, ko da yake ya zuwa yanzu ba su san wane irin sinadari ne da ke cikin kofi ya sa hanji kara yin aiki ba, amma sakamakon nazarinsu ya shaida cewa, akwaia bukatar kara yin nazari kan mutane domin tabbatar da cewa, ko shan kofi zai taimaka wa mutanen da suke fama da matsalar rashin zuwa bayin gida ko kuma toshewar hanji bayan da aka yi musu tiyata, ko a’a. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan