logo

HAUSA

Watakila kofi yana taimaka wa mutane rage kiba

2021-02-02 15:42:24 CRI

Watakila kofi yana taimaka wa mutane rage kiba_fororder_src=http___5b0988e595225.cdn.sohucs.com_q_70,c_zoom,w_640_images_20180807_51f3168a270d434daa7f48027f3fd2cc.jpeg&refer=http___5b0988e595225.cdn.sohucs

Wani sabon nazari da aka gudanar a jami’ar Nottingham ta kasar Birtaniya ya nuna mana cewa, kofi zai kara azama kan yadda Brown fat ya kara yin aiki a jikin dan Adam, ta yadda zai taimaka wajen samun daidaiton nauyin jikin dan Adam.

Mene ne Brown fat? Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, akwai nau’o’in kitse guda 2 a cikin jikin dan Adam, wato White fat da Brown fat. White fat, nan ne ake adana karfi a ciki, yana da nasaba da matsalar kiba. Brown fat, wani curin kitse ne dake daidaita yanayin jikin dan Adam, yana kuma kara azama kan jikin dan Adam kan yadda zai yi amfani da sukari da White fat wajen samar da zafi, a kokarin kare jikin dan-Adam daga illar sanyi. Idan Brown fat ya kara yin aiki, to, za a samu daidaiton yawan sukari da kitse cikin jinin dan Adam, kana kuma hakan zai taimaka wajen rage kiba.

Masu nazari daga jami’ar Nottingham ta kasar Birtaniya sun yi nazari zurfi kan kwayoyin halitta, inda suka gano cewa, sinadarin Caffeine yana sa kaimi kan Brown fat, don haka sun yi zaton cewa, za su yi nazarin kan sauyarwar yawan Brown fat da ke jikin dan Adam bayan da mutum ya sha kofi.

Rahotanni na nuna cewa, akwai Brown fat da yawa a wuyan mutane. Wannan ya sa masu nazarin su ka gayyaci masu aikin sa kai, don su sha kwaf na kofi, daga baya an dauki hoton wuyansu kan ta hanyar amfani da fasahar zamani dake aikewa da zafi. Masu nazarin sun gano cewa, sassan wuyan masu aikin sa kan inda ake fi samun Brown fat sun kara yin zafi.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, wannan ne karo na farko da nazarin da aka gudanar kan jikin dan Adam ya shaida cewa, shan kwaf guda na kofi, yana sa kaimi kan Brown fat da ke cikin jikin dan Adam. Amma duk da haka, akwai bukatar ci gaba da nazari kan wadanne sinadarai ne da ke cikin kofi ya yi tasiri kan Brown fat, kana baya da sinadarin Caffeine, ko akwai wasu sinadarai wadanda suke yin tasiri kan Brown fat.

Matsalar kiba, ta dade tana addabar jama’a a zamanin yau. Wannan sakamakon nazarin ya taimaka wajen daidaita nauyin jikin dan Adam da kuma daidaita yawan sukari a cikin jinin dan Adam. Yana kuma taimakawa mutane yaki da matsalar kiba, ciwon sukari da sauran cututtuka dake da nasaba da wadannan. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan