logo

HAUSA

Yadda Amurka Take Kallon Kasar Sin Daidai Yana Da Muhimmanci Wajen Kyautata Hulda A Tsakanin Kasashen 2

2021-02-02 21:37:35 CRI

Idan mun waiwayi hulda da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka cikin shekaru 4 da suka gabata, to za mu iya fahimtar cewa, saboda wasu ’yan siyasar Amurka sun mayar da kasar Sin a matsayin ’yar takarar kasarsu, bisa manyan tsare-tsare, sun yi kuskure kan manufofin Amurka game da kasar Sin, don haka huldar da ke tsakanin kasashen 2 ta taba shiga mawuyacin hali, lamarin da ya illata zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Yadda Amurka take kallon kasar Sin yadda ya kamata, wani sharadi ne na farko ga sabuwar gwamnatin Amurka, wajen tsara manufofinta game da kasar Sin. haka kuma yana da muhimmanci matuka wajen kyautata hulda a tsakanin kasashen 2.

Yau Talata 2 ga wata, Yang Jiechi, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS, kuma darektan ofishin kula da harkokin diflomasiyya na kwamitin tsakiya na JKS, ya tattauna ta kafar bidiyo da mambobin kwamitin raya dangantaka tsakanin Amurka da Sin, inda ya ba da shawara kan yadda za a farfado da huldar da ke tsakanin kasashen 2. Yang ya yi fatan cewa, Amurka za ta yi watsi da tunanin cin moriya da faduwar wani, ta rika kallon kasar Sin ta hanyar da ta dace, ta kuma hada kai da kasar Sin wajen raya huldar da ke tsakaninsu yadda ya kamata.

A halin yanzu, Sin da Amurka za su iya fadada hadin gwiwarsu a fannonin yaki da annobar COVID-19, da farfado da tattalin arziki, da sauyin yanayi da dai sauransu.

Kamata ya yi sabuwar gwamnatin Amurka ta yi kokari tare da Sin wajen farfado da huldar da ke tsakanin kasashen 2. Tarihi zai sake nuna cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Amurka, buri ne na bai daya na al’ummomi, kuma wanda zai tafi da zamani, wanda ba za a iya dakatar da shi ba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan