logo

HAUSA

Rayukan Amurkawa na fuskantar babbar barazana sakamakon tsarin kiwon lafiyar kasar

2021-01-17 21:53:46 CRI

Rayukan Amurkawa na fuskantar babbar barazana sakamakon tsarin kiwon lafiyar kasar_fororder_A

A lokacin da cutar mashako ta COVID-19 ke ci gaba da yaduwa a duniya, an kara fahimtar ainihin tsarin kiwon lafiya na kasar Amurka, wato bautawa masu hannu da shuni, da kawo barazana ga rayukan mutanen kasar.

A kasashen Turai da kasar Japan, tsarinsu na inshorar kiwon lafiya yana shafar dukkanin al’ummu, amma a kasar Amurka, an hada tsarin inshorar kiwon lafiya na kasuwanci da irin na gwamnati tare. Harkokin kiwon lafiya na Amurka suna dogara kusan kacokan kan kasuwanni, a maimakon gwamnati.

Rayukan Amurkawa na fuskantar babbar barazana sakamakon tsarin kiwon lafiyar kasar_fororder_B

Dogaro kan kasuwa fiye da kima, gami da rashin sa ido daga gwamnati, ya sa tsarin kiwon lafiyar Amurka ya zama tamkar wurin da ake kokarin neman samun moriya. Alal misali, akwai wasu manyan kamfanonin hada magunguna na Amurka wadanda suka yi babakere a kasuwannin magungunan kasar, al’amarin da ya sa kasar ta zama daya daga cikin kasashen dake fama da tsadar magunguna a duk fadin duniya.

Bayan barkewar cutar COVID-19, duk da cewa akwai inshorar kiwon lafiya, amma mutanen da suka kamu da cutar wadanda ba su da sauran cututtukan dake da alaka da ita, kamata ya yi su biya kudin da matsakaicinsa ya kai dala 9800 don ganin likita. Amma idan an kamu da cutar, sa’annan ana kuma fama da sauran wasu cututtukan dake da alaka da ita, yawan kudin ganin likita da za a kashe zai zarce dala dubu 20. A saboda haka, binciken jin ra’ayoyin jama’a ya nuna cewa, daga cikin mutane 11 da suka kamu da cutar COVID-19 a Amurka, akwai guda daya wanda ya ki zuwa ganin likita saboda tsada.

Rayukan Amurkawa na fuskantar babbar barazana sakamakon tsarin kiwon lafiyar kasar_fororder_C

A yayin da mutanen Amurka ke fama da tsadar ganin likita da na magani, masu ruwa da tsaki suna ta kashe makudan kudade a asirce. Suna amfani da kudaden da suka kwace a fannin siyasa, domin hukumomin tsara dokoki gami da manufofin kiwon lafiya su tsara manufofin daidai bisa moriyarsu, ta yadda za su kara samun babbar moriya. (Murtala Zhang)