logo

HAUSA

Salon cin abinci na Mediterranean ya taimaka wajen yin rigakafin kamuwa da cutar Alzheimer's disease

2021-01-18 11:29:41 CRI

Salon cin abinci na Mediterranean ya taimaka wajen yin rigakafin kamuwa da cutar Alzheimer's disease_fororder_src=http___image.uczzd.cn_1803494213748605875&refer=http___image.uczzd

Kwanan baya, ma’aikatar abinci da aikin gona ta kasar Jamus ta shirya wani taron bita, inda kwararru suka tattauna kan alakar da ke tsakanin salon cin abinci da kamuwa da cutar Alzheimer's. Wasu kwararru suna ganin cewa, salon cin abinci na yankin Mediterranean ya taimaka wajen kare mutane daga kamuwa da cutar ta Alzheimer's. Amma sun yi nuni da cewa, salon cin abinci yana daya daga cikin dalilan da sukan yi tasiri kan kamuwa da cutar.

Mene ne cutar Alzheimer's? Ita ce wani nau’in ciwon karancin basira da dake farawa daga matsalar mantuwa, daga bisani ta shafi tunanin mutane da kwarewar magana har ma da gudanar da harkokin yau da kullum. Kwararru daga kasar Jamus sun yi bayani da cewa, salon cin abinci na Mediterranean ya taimaka wajen kare mutane daga kamuwa da cutar ta Alzheimer's, hakan da ya nuna cewa, dole ne a kara cin kayayyakin lambu da naman kifi da naman kaji da naman agwagwa da makamantansu, tare da rage cin naman sa, naman rago da naman alade.

Mene ne ma’anar salon cin abinci na Mediterranean? Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, salon cin abinci irin na Mediterranean, wani nau’in salon cin abinci ne da ake bi a wasu wuraren da ke bakin tekun Mediterranean. A wadannan wurare, mutane su kan ci kayayyakin lambu, ‘ya’yan itatuwa, kifi, dangin kyada da man zaitun da sauran man girke da ake sarrafawa daga tsirrai.

Wasu kwararrun da suka halarci taron sun bayyana cewa, idan ba a ci abinci kamar yadda ya kamata ba, to, za a kara fuskantar barazanar kamuwa da cutar ta Alzheimer's, da samun kiba, kamuwa da cutar sukari mai nau’in 2, cututtukan zuciya da na magudanar jini.

Duk da haka, kwararrun sun kuma jaddada cewa, salon cin abinci, yana daya daga cikin dalilan da sukan yi tasiri kan kamuwa da cutar. Ya zuwa yanzu ba a tabbatar da wani nau’in abinci na musamman ne ke iya kare mutane daga kamuwa da cutar Alzheimer's ba tukuna.

Alkaluma sun nuna cewa, a shekarar 2018, akwai mutane miliyan 1 da dubu 700 da suka kamu da cutar Alzheimer's a kasar Jamus. Idan ba a samu ci gaba wajen shawo kan cutar ba, to, an kiyasta cewa, yawan masu fama da cutar zai kai miliyan 3 a shekarar 2050.

Kwararrun sun ba da shawarar cewa, ya dace tsoffafi su kyautata salonsu na cin abinci, su kara cin kayayyakin lambu, ‘ya’yan itatuwa, kifi da hatsin da ba a sarrafa sosai ba, a kokarin kyautata lafiyarsu. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan