logo

HAUSA

Sin ta soki matakin Amurka na aikewa Taiwan sako maras kyau game da batun cinikin makamai

2020-11-04 19:49:59 CRI

Kakakin ma'aikatar wajen Sin Wang Wenbin, ya ce Sin na matukar adawa da matakin Amurka, na aikewa Taiwan mummunan sako mai hadari, na amince ta sayarwa yankin na Taiwan jiragen saman yaki marasa matuka. Wang Wenbin ya ce Sin za ta dauki matakin da ya dace, gwargwadon sauyawar yanayin da ake fuskanta. A jiya Talata ne dai hukumar tsaron Amurka ta Pentagon, ta bayyana cewa, ma'aikatar wajen kasar ta amince da shirin sayarwa Taiwan wasu jiragen saman yaki marasa matuka na zamani guda 4, kuma tuni aka aikewa majalissar dokokin Amurkar sakon sanar da matakin a hukumance. To sai dai kuma, kasar Sin ta bayyana wannan mataki a matsayin abun da ya keta hurumin manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da ma rahotanni 3 da kasashen biyu suka cimma, suka kuma fitar da takardar amincewa da su. Kaza lika Sin na kallon matakin a matsayin tsoma bakin Amurka ciki harkokin gidan Sin, wanda hakan ke matukar tauye ikon Sin na mulkin kai, da tsaro da kuma moriyar ta.

Jami'in ya kuma ce, Sin na gargadin Amurka da ta dakatar da wannan yunkuri na sayarwa Taiwan makamai, da sauran huldodi na soji, kana ta haramta duk wani shiri na yin hakan a nan gaba. (Saminu)