logo

HAUSA

Wannan Al'ada Ta Tsawon Shekaru 31 Ta Kara Bayyana Irin dadadden Zumuncin Dake Tsakanin Sin Da Afirka

2021-01-06 13:37:43 CRI

Yanzu haka ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi yana ziyarar aiki a kasashe 5 na Afirka, ciki had da Nijeriya, Congo(Kinshasa), Botswana, Tanzaniya da Seychelles. Wannan shi ne karo na 31 da ministan harkokin wajen kasar Sin ya fara ziyarar aiki a kasashen Afirka a farkon wata sabuwar shekara tun shekarar 1991. A daidai lokacin da cutar numfashi ta COVID-19 take ci gaba da addabar kasashen duniya, wannan al’ada da aka shafe tsawon shekaru 31 ana bi, ta kara bayyana irin dadadden zumuncin da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, wadanda suke jure wahala kafada da kafada, da kuma mara wa juna baya,tamkar‘yan uwan juna ne.

Yadda duk wani ministan harkokin wajen kasar Sin ya kan fara ziyarar aiki a kasashen Afirka a farkon kowace shekara, ta kara shaida dankon zumuncin da ke tsakanin Sin da Afirka. Shekarar 2020, shekaru 20 ke nan da kafuwar taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC. A cikin shekaru 20 da suka wuce, dandalin FOCAC ya tafi daidai da ci gaban zamani, inda aka rungumi zaman lafiya, ci gaba da hadin kai. Ya kuma ba da jagora kan yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka. FOCAC, wani abin misali ne wajen cudanyar sassa daban daban da kuma tsayawa kan samun nasarar moriyar juna.

A yayin da ake fama da cutar Covid-19, kasar Sin da kasashen Afirka sun hada kan juna wajen tinkarar annobar. A lokacin da kasar Sin ta fi fuskantar mawuyancin hali na yaki da annobar, shugabanni fiye da 50 na kasashen Afirka, sun aika da sakonni ko sanarwa don nuna jaje da goyon baya ga kasar Sin. Kana a lokacin da annobar ta barke a nahiyar Afirka, ita ma kasar Sin ta aikawa kasashen Afirka kayayyakin yaki da annobar masu yawa, tare da aika tawagogin ma’aikatan lafiya zuwa kasashen Afirka fiye da 10. Ta kuma daddale yarjejeniya tare da kasashe 12 na Afirka don dakatar da biyan bashi, baya ga rage da soke basusukan da take bin kasashe 15 na Afirka ba tare da biyan kudin ruwa ba, wadanda ya kama su biya bashin a karshen shekarar 2020. Adadin da ya fi na kasashe mambobin kungiyar G20 yawa. Har ila yau, kasar Sin ta cika alkawarin da ta yi a taron kolin musamman na hadin kan Sin da kasashen Afirka wajen yaki da annobar, inda ta fara aikin gina hedkwatar cibiyar dakile da kandagarkin cututtuka masu yaduwa ta Afirka a karshen shekarar 2020 kafin lokacin da aka tsara.

Shawarar “ziri daya da hanyan daya” da kasar Sin ta gabatar da kuma manyan matakai guda 8 da shirye-shirye guda 10 dangane da yin hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, dukkansu sun mai da hankali kan batun ci gaba. Kasar Sin ta taimaka wa kasashen Afirka wajen shimfida hanyoyin dogo da tsawonsu ya kai kilomita fiye da dubu 6, da hanyoyin mota masu tsawon kilomita dubu 6, da gina tasoshin jiragen ruwa kusan 20 da manyan tashoshin samar da wutar lantarki fiye da 80. Tun bayan kafuwar FOCAC a shekarar 2000 har zuwa yanzu, cinikayya a tsakanin Sin da Afirka ta ninka har sau 20, kana kuma jarin da kasar Sin take zuba wa Afirka kai tsaye ya ninka har sau 100.

A cikin sabuwar shekarar da muke ciki, kasar Sin da kasashen Afirka za su samu sabuwar damar yin hadin gwiwa. A yayin ziyarar da Wang Yi yake yi a Afirka, ana fatan zai tattauna da kasashen Afirka kan fannoni daban daban, a kokarin goyon bayan kasashen Afirka yaki da annobar, farfado da tattalin arziki, kara azama kan aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, da raya al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a tsakanin Sin da Afirka. A ranar 1 ga watan Janairun bana ne, aka kaddamar da yankin ciniki cikin ‘yanci na Afirka, wanda ya kunshi kasashe 54 da al’ummomi biliyan 1.2, lamarin da ya samar wa Sin da Afirka sabuwar damar yin hadin gwiwa ta fannonin tattalin arziki da ciniki. Kamfanonin kasar Sin za su kara ba da nasu taimako wajen raya masana’antun Afirka ta hanyar zuba jari.

A bana za a kaddamar da sabon taron FOCAC a kasar Senegal, inda bangarorin 2 za su tattauna batutuwan allurar rigakafin cutar ta COVID-19, farfadowar tattalin arziki da sauya hanyar raya tattalin arziki, a kokarin bude wani sabon babi na hada kan Sin da Afirka domin samun moriyar juna da nasara tare. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan