logo

HAUSA

Liu Guijin: Ziyarar ministan harkokin wajen Sin a Afirka ta shaida muhimmancin da Sin ke dorawa kan raya dangantaka tsakanin bangarorin biyu

2021-01-04 13:47:48 CRI

Daga ranar 4 zuwa 9 ga wata, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi zai ziyarci Tarayyar Najeriya, Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo, Botswana, Tanzaniya da ma Seychelles bisa gayyatar da aka yi masa. Yayin da Liu Guijin, tsohon jadakan Sin da ke kasar Afirka ta Kudu kuma wakilin musamman na farko na gwamnatin Sin kan harkokin Afirka ke zantawa da wakiliyar babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG, ya bayyana cewa, a lokacin da aka fuskanci yaduwar annobar COVID mai saurin yaduwa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan cudanya da tattauna da kasashen Afirka fuska da fuska, lamarin da ya shaida sahihanci da kauna da Sin ke nunawa Afirka, da ma yadda Sin ke dora muhimmanci kan Afirka da raya dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu a ko da yaushe.

Tun daga shekarar 1991, ministocin harkokin wajen kasar Sin suke bin al’adar kai ziyara Afirka a farkon ko wace sabuwar shekarar, a wannan shekarar ta 2021 ma, ana yin hakan duk da fama da yaduwar cutar COVID-19 a fadin duniya.

Game da wannan batu, Liu Guijin, tsohon jadakan Sin da ke kasar Afirka ta Kudu kuma wakilin musamman na farko na gwamnatin Sin kan harkokin Afirka ya bayyana cewa, ban da kasar Sin, babu wata kasa da ke iya yin hakan, lamarin da ya shaida matukar muhimmancin da kasar Sin ke nuna wa Afirka a ko da yaushe. Yana mai cewa,

“Ban da kasar Sin, babu wata kasa da ministocin harkokin wajenta ke kai ziyara kasashen Afirka a farkon ko wace shekara, a cikin shekaru fiye da 30 da suka gabata, wannan ba wai riya ba ce, abu ne da ya zama al’ada, lamarin da ya shaida yadda Sin ke mayar da hankali kan Afirka da ma dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu. Ban da wannan kuma, lamarin da ya shaida cewa, ko da yaushe Sin na tsayawa kan manufar ‘kulla dangantaka da kasashen Afrika bisa gaskiya da kauna da nuna yarda da aminci, kamar yadda ake gaisawa da dangogi, a kowa ne irin hali, za a ci gaba da martaba wannan al’ada. Hakika babu kasashen da za su iya yin hakan, sai kasar Sin.”

A ziyarar da minista Wang Yi zai kai kasashen Afirka a wannan karo, zai ci gaba da martaba manufar “kulla dangantaka da kasashen Afrika bisa gaskiya da kauna da nuna yarda da aminci” da kuma dabarar “cimma muradu da martaba ka’idoji”, wajen tattaunawa da bangaren Afirka kan inganta hadin gwiwarsu, a kokarin aiwatar da muhimman ra’ayoyin bai daya da shugabannin Sin da kasashen Afirka suka cimma da ma sakamakon da aka samu a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afirka na FOCAC gami da taron koli na musamman kan hadin kan Sin da Afirka kan yaki da COVID-19, ta yadda za a mara wa kasashen Afirka baya wajen yaki da annobar, da farfado da tattalin arziki, da sa kaimi ga ci gaban Sin da Afirka bisa shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kuma raya kyakkyawar makomar bangarorin biyu ta bai daya.

Haka zakila, Liu Guijin ya nuna cewa, a farkon bullar cutar COVID-19, kasashen Afirka da dama sun ba da tallafin kayayyaki da kudi ga kasar Sin, da karawa Sin kwarin gwiwa ta hanyoyi daban daban. Bayan cutar ta bulla a Afirka kuma, yayin da Sin ke kokarin dakile yaduwar cutar a cikin gidanta, ta samar wa Afirka taimako da goyon baya da dama ba tare da bata lokaci ba, lamarin da ya shaida hadin kai da taimakon juna dake tsakanin bangarorin biyu. Liu ya kara da cewa,

“Bayan da kasar Sin ta takaita yaduwar cutar COVID-19, ta tura tawagogin ma’aikatan lafiya da dama zuwa Afirka, da samar musu da kayayyakin rigakafi, baya ga kiran taron koli na musamman da shugaban kasar Sin ya yi kan hadin kan Sin da Afirka wajen yaki da cutar. Hakaki wannan ya nuna irin kaunar da ke tsakanin Sin da Afirka da taimakon da suke bai wa juna.”

Shekarar 2021, shekara ce da ta tantance sakamakon da aka samu a gun taron koli na Beijing na dandalin FOCAC. Liu Guijin ya furta cewa, daga shekarar bana, dandalin FOCAC ya kama hanyar shiga shekaru 30. Annobar COVID-19 ta kawo illa sosai ga duniya, yadda za a inganta hadin kan Sin da Afirka bisa wannan yanayin da ake ciki, da ma shirya taron ministoci karo na 8 na dandalin FOCAC yadda ya kamata, na daga cikin muhimman batutuwa da za a mai da hankali a kai. Liu ya ce,

“Bisa wannan yanayin da muke ciki, yadda za a tinkari kalubalolin da ke gabanmu, da inganta hadin kan tattalin arziki da cinikayya, da farfado da tattalin arziki bayan annobar, da kirkiro hanyar bunkasuwa, dukkansu muhimman fannoni ne da za a tattauna don kyautata hadin gwiwa a kai. Don haka, za mu mayar da hankali kan taron ministoci na karo na 8 karkashin inuwar FOCAC da za a kira a watanni shida na karshen shekarar bana a kasar Senegal.”(Kande Gao)