logo

HAUSA

Kasar Sin na goyon bayan komawar 'yan gudun hijirar Syria gida

2020-11-12 11:44:58 CRI

Jakadan Sin a Syria, Feng Biao, ya ce kasarsa na goyon bayan komawar ‘yan gudun hijirar Syria gidajensu.

Feng Biao, ya bayyana haka ne ga kamfanin dillancin labarai na kasar Sin na Xinhua, lokacin bude taron kasa da kasa kan ‘yan gudun hijira da aka yi jiya a birnin Damascus, da nufin karfafawa ‘yan gudun hijirar Syria gwiwar komawa kasarsu.

Sai dai, jakadan ya bayyana wasu sharuda 3 da ya kamata a cimma kafin komawar ta su.

Da farko, samar da mafita ga rikicin kasar a Siyasance. Na biyu, taimakawa Syria sake gina tsarin tattalin arzikinta. Na uku kuma, kawo karshen ta’addanci domin samun yanayi mai aminci na komawar ‘yan gudun hijirar.

Kimanin kasashe 27 da kungiyoyi ko hukumomi 12 ne suka shiga taron na yini biyu da nufin tattaunawa kan kokarin saukaka komawar ‘yan gudun hijirar Syria, kasaru na asali. (Fa’iza Mustapha)