Kasashen duniya sun yi Allah wadai da kisan masanin kimiyar nukiliya na kasar Iran
2020-12-01 11:10:22 CRI
Kasashe da dama, ciki hadda Jamus da Rasha da AL da Labanon da dai sauransu, sun yi Allah wadai da kisan da aka yi wa masanin kimmiyar nukiliya na kasar Iran, Mohsen Fakhri Zadeh a kwanakin baya, yayin harin da aka kai masa a wani wurin dake dab da birnin Tehran fadar mulkin kasar.
Ministan tsaron kasar Amir Hatami ya halarci jana’izar da aka yi a jiya Litnin tare da bayyana cewa, Iran ba za ta yi biris da wadannan mumunan laifufuka ba, inda ya ce za ta yi iyakacin kokarin cafke wadanda suka aikata laifin, domin gurfanar da su a gaban kuliya tare da yanke musu hukunci. (Amina Xu)