logo

HAUSA

Aikin na’urar binciken duniyar wata ta Chang'e-5 yana da babbar ma’ana

2020-11-24 19:12:57 CRI

Aikin na’urar binciken duniyar wata ta Chang'e-5 yana da babbar ma’ana

Da safiyar yau Talata 24 ga wata, da misalin karfe 4 da rabi agogon birnin Beijing, kasar Sin ta yi nasarar harba na’urar binciken duniya wata ta Chang’e-5, wannan mataki shi ne na uku da kasar Sin ta cimma, yayin harba na’urar binciken duniyar wata da ba ta dauke mutum, a karo na farko, na’urar za ta dawo doron duniya tare da tabon duniyar wata na farko.

Hakika na’urar Chang’e-5 za ta gudanar da wasu ayyuka a karo na farko, alal misali, za ta dauko wasu samfura daga gefen duniyar wata da kanta, kuma za ta shiga hanyar tafiyarta dake da nisan kilomita dubu 380 daga duniyarmu da kanta, kana za ta dawo doron duniya da tabon duniyar wata cikin tafiyar kilomita 11.2 cikin dakika daya.

Kawo yanzu kasashen Amurka da tsohuwar tarayyar Soviet ne kawai suka taba tace tabon duniyar wata da wasu samfuran duwatsu, wadannan samfura sun sabunta ilimin bil Adama game da asalin duniyar wata da doron duniyarmu da kuma duniyar rana.

A wannan karo kuma, na’urar Chang’e za ta dauko tabo kusan kilo 2 a wuraren da sauran na’urorin bincike ba su taba zuwa ba, an lura cewa, tun daga ranar 18 ga watan Agustan shekarar 1976 wato bayan da na’urar binciken dunyar wata da tsohuwar tarayyar Soviet ta harba ta dauko samfura daga duniyar wata, har zuwa yanzu bil Adama bai taba samun sabbin samfura daga duniyar wata a cikin shekaru 44 da suka gabata ba.

A don haka masana kimiyya da fasaha na kasashen duniya, suna sa ran kasar Sin za ta samu babban sakamako a wannan karo, masanin bayanan kasa na jami’ar Munter na kasar Jamus Carolyn Van Der Bogert ya bayyana cewa, yana da wahala bangaren fasaha ya dawo da samfuran duniyar wata doron duniyarmu, shehun malamin dake aiki a hukumar zirga-zirgar sararin samaniya ta Turai dake birnin Noordwijk na kasar Netherlands James Carpenter shi ma ya bayyana cewa, aikin da na’urar binciken Chang’e ke gudanarwa, yana da babbar ma’ana ga aikin binciken duniyar wata na bil Adama.

Kana shugaban kungiyar tsangayar duniyar wata, ‘dan asalin kasar Italiya Giuseppe Reibaldi ya yi tsokaci cewa, sakamakon da kasar Sin ta samu a bangaren kimiyya da fasahar binciken sararin samaniya, zai amfanawa daukacin kasashen duniya, saboda makasudin binciken sararin samaniya na kasar Sin shi ne domin biyan bukatun sha’awar bil Adama, gami da neman dabarun raya bil Adama a nan gaba.(Jamila)