Da yake zantawa da Xinhua a gefen taron karshen mako na shekara-shekara kan muhimman batutuwa da suka shafi nahiyar Afrika na gidauniyar Mo Ibrahim, Abdalla Hamdok ya ce matasa 'yan kasa da shekaru 25 ne suka mamaye kaso 60 na al'ummar nahiyar, kuma kawo shekarar 2050, nahiyar za ta dauki mutane miliyan 452 'yan kasa da shekaru 25.
Ya ce karfin wadanan matasa da burinsu da abubuwan da za su iya zai ba kasashen Afrika kadarar da ba sa taba gani ba.
Abdalla Hamdok wanda kuma shi ne shugaban majalisar bada shawara ta gidauniyar, ya ce galibin matasan Afrika na shafe shekaru da dama a makaranta, amma kuma ba sa samun fasahohin da suka kamata, wanda ci gaban tattalin arziki ke bukata, abun da ke barazana ga bunkasar nahiyar.
Ya kuma yi kira ga dukkanin kasashen Afrika su samarwa da matasa ilimi da fasahohin da suka dace, domin ba su damar kai wa ga cimma ajandar nahiyar ta sauya fasalin tattalin arziki.
A cewar wani rahoton nazarin tattalin arziki na bankin raya Afrika, ya ce ana sa ran karuwar al'ummar Afrika zai kara yawan kudin da ake kashewa na sayen kayayyakin amfani daga dala biliyan 680 a 2008 zuwa dala triliyan 2.2 a shekarar 2030. (Fa'iza Mustapha)