Shi dai Mr Tillerson ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a yayin karkare ziyararsa ta aiki ta farko da ya kai kasashen Afrika.
A rangadin da ya kai wasu kasashen Afrika 5, Tillerson ya gargadi kasashen Afrika da su yi taka-tsantsan da kasar Sin domin gudun kada kasar ta Sin ta kwace ikon tafiyar da harkokin kasashen su ko kuma don gudun kada ta haddasa musu rikicin basuka mai nauyin gaske.
Da yake mayar da martani, jakadan na Sin ya bayyana cewa, kasar Sin da kamfanoninta sun zuba jarin sama da dala biliyan 100 a fadin nahiyar, ta kuma gina layin dogo sama da kilomita 6,500, da manyan titunan mota 6,000, da makarantu 200 da kuma filayen wasanni kimanin 80.
Ya kara da cewa, kasar Sin ta samar da ayyukan yi, ta yi musayar kwarewa, da fasahohin zamani, kana ta sauya rayuwar al'ummomin Afrika masu yawan gaske.
Lin ya ce, wata kila ma Tillerson ya sauka a tashar jirgin da kasar Sin ta samar da kudaden aikinsa, ko kuma ya yi amfani da titunan motar da aka gina da tallafin kasar Sin, kana ko kuma ya yi tsokaci ga filin wasan da aka gina bisa hadin gwiwar kasar Sin da Afrika.
"Abin da kawai suke bukata shi ne a cigaba da barin Afrika irin yadda take, a barta cikin talauci, da rarrabuwar kai, kuma suna son a ko da yaushe a dinga juya akalar kasashen irin yadda aka ga dama. Abin da suke bakin ciki da shi shine yadda Afrika take samun 'yanci ta fuskar cigaban tattalin arziki, ta hanyar taimakon da kasar Sin ke bayarwa. Abinda ke damunsu shine yadda Afrika ke samun karfi ta yadda babu wanda ya isa ya juya akalarta a siyasance" in ji jakadan na Sin. (Ahmad Fagam)