An dai yi wannan kira ne a yayin taron yini uku, game da bunkasa rayuwar matasan Afirka a birnin Addis Ababan kasar Habasha, taron dake da nufin zakulowa matasa dabarun bunkasa samar da ayyukan yi, da raya sana'o'i da kirkire kirkire.
Wata kididdiga ta baya bayan nan da bankin raya Afirka na AfDB ya fitar ta nuna cewa, akwai zunzurutun matasa a nahiyar Afirka kimanin miliyan 480, adadin da ake hasashen zai kai ga miliyan 850 nan da shekarar 2050.
Taron dai na wannan karo na da mahalarta daga kasashen Afirka 47, da masana a fannin tsara manufofi, da masu samar da guraben ayyuka, da abokan hulda na kasa da kasa a fannin.
Kaza lika za kuma a yi musayar managartan ra'ayoyi, game da yaki da rashin ayyukan yi, da karancin su, da ma sauran batutuwa masu alaka da hakan.(Saminu Alhassan)