Masu rajin, sun bayyana haka ne yayin taron nahiyar kan ilimi dake gudana a birnin Nairobin Kenya.
Wani babban jami'i a Kungiyar raya ilimi a Afrika Makha Ndao, ya ce wajibi ne a yi amfani da sabon tsarin na samar da kudaden don taimakawa shirye-shiryen inganta ilimi da fasahohi a Afrika.
Ya ce ya kamata a mayar da hankali ga samar da kudi ga bangaren ilimi a nahiyar, la'akari da yadda tallafin da ake samu daga al'ummomin kasashen waje ke raguwa.
A cewar MDD, nahiyar Afrika na bukatar karin dala biliyan 40 domin cimma muradi na 4, dake cikin muradun ci gaba masu dorewa kan ilimi, ya zuwa 2030.
Masu rajin sun kuma bukaci gwamnatocin Afrika su maganace duk wasu manufofi dake tarnaki ga samar da isasshen kudi ga bangaren ilimi. (Fa'iza Msutapha)