Kwamitin sulhu na MDD ya bada sanarwa a ranar 11 ga wata, inda ya yi zargi da kakkausar murya kan harin da 'yan ta'adda suka kaiwa rundunar kiyaye zaman lafiya a jamhuriyar Afrika ta tsakiya.
An bada labari cewa, a ranar Litinin 10 ga wata 'yan bindiga sun yi musanyar wuta a birnin Bangui, hedkwatar kasar Afrika ta tsakiya da rundunar, lamarin ya haddasa mutuwar wani soja mai kiyaye lafiya dan kasar Rwanda yayin da wasu 8 suka ji rauni. Sanarwar kuma ta nuna juyayi sosai ga iyalin mamatan tare da jajantawa iyalan sojojin da suka ji rauni tare da yi musu fatan samun sauki cikin hanzari.
Ban da wannan kuma, sanarwar ta ce, kwamitin ya nuna goyon baya ga kokarin da rundunar gwamnatin kasar suke yi na kiyaye zaman lafiyar Bangui da fararen hularta, kuma tana bukatar dakarun da su daina yin amfani da karfin tuwo wajen kwantar da hankula a kasa don samun damar shiga shirin shimfida zaman lafiya ba tare da gindaya wani sharadi ba. (Amina Xu)