An yi wannan kira ne yayin wani taron yini biyu kan ilimi da aka fara a jiya, jajibirin ranar matasan Afrika dake gudana yau Laraba 1 ga watan Nuwamba, wanda Sashen kula da jama'a da kimiyya da fasaha na hukumar AU tare da hadin gwiwar kungiyar kawance don raya nahiyar Afrika NEPAD da sauran wasu kungiyoyi suka shirya.
Taron na mai da hankali ne kan samar da ingantaccen ilimi a matsayin hanya ta kawo karshen rashin aikin yi a Afrika.
Tarayyar Afrika na bikin wannan rana a kowacce shekara, inda take tara matasa daga dukkan shiyyoyin nahiyar 5, da ma wadanda ke zaune a kasashen waje, domin su kara jadadda kudurinsu na shiga a dama da su wajen aiwatar da kunshin ajanda ta 2063, wadda ke burin ganin al'ummar Afrika sun raya nahiyar tare da tabbatar da zaman lafiya da hadin kai da kuma samar da wani adadi na masu aikin yi a duniya.
A cewar shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahamat, a watan Mayun da ya gabata yawan al'ummar Afrika ya kai sama da biliyan 1.2 da matsakaicin shekaru 19 da rabi
Ya kara da cewa, Afrika ita ce nahiya ta biyu dake da yawan al'umma bayan nahiyar Asia, kuma ita ce nahiya dake da karancin matasa masu aiki, ya na mai cewa abu ne mai muhimmanci amfani da wannan yawan a matsayin hanya ta samar da sauyi da ci gaba. (Fa'iza Mustapha)