in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai bukata Afrika ta sanya matasa cikin shirye shiryen raya ci gabanta
2017-06-22 10:12:12 cri

Kasancewar akwai kusan kashi 35 ciki 100 na matasan nahiyar Afrika wadanda ba su da takamammiyar sana'ar dogaro da kai, wani jami'in kungiyar tarayyar Afrika ya bukaci gwamnatocin kasashen su tabbatar sun shigar da matasan cikin muhimman ayyuka ta yadda za su ba da gagarumar gudunmowa wajen ci gaban kasashen nasu.

Minata Samate Cessouma, kwamishinan sashen kula da al'amurran siyasa na kungiyar tarayyar Afrikar ya bayyana hakan ne a lokacin bikin ranar ma'aikatan gwamnati ta Afrika da aka gudanar a Kigalin babban birnin kasar Ruwanda, ya ce, ya kamata gwamnatocin nahiyar Afrika su yi garambawul game da shirinsu na ba da ilmi da ba da horo ta yadda matasan za su samu damar kwarewa don su samu sana'o'in dogaro da kansu.

Bikin ya samu halartar sama da mutane 500.

Da yake jagorantar bude taron, firaiministan kasar Ruwanda Anastase Murekezi, ya jaddada muhimmancin horas da matasa a fannonin raya ci gaban tattalin arziki da zaman takewar al'umma.

Ya ce, kamata ya yi a baiwa matasan damammaki don su ba da gudumowarsu, kuma wajibi ne gwamnatoci su horas da matasan ta yadda kwarewar da suka samu za ta dace da bukatun da ake da su a wuraren aikin domin su samu zarafin aiwatar da ayyuka masu inganci bisa ga kwarewa a guraben aikin da suka tsinci kansu ciki.

Ana gudanar da bikin ne a ranar 23 ga watan Yunin a kasashen mambobin na AU domin nuna yabo ga rawar da ma'aikatan gwamnati ke takawa wajen ci gaban al'umma.

Ana gudanar da bikin ranar ma'aikatan gwamnati na Afrika ne bayan shekaru biyu biyu wanda mambobin kungiyar AU ne ke daukar nauyin bikin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China