Da zarar Amurka ta kaddamar da takardar sunayen kayayyaki kirar kasar Sin da ta shawarci a kara haraji a kai bisa sakamakon bincike mai lamba 301, sai kasar Sin ta sanar da matakin daukar fansa na kara haraji. Ga alama matsalar ciniki dake tsakanin kasashen 2 ta tsananta.
Yau Alhamis wasu masanan kasar Sin sun bayyana a nan Beijing cewa, nufin Amurka na yin haka shi ne domin kawo illa ga shirin kasar Sin wato "Kirar kasar Sin 2025". Ta yi yunkurin raunana injuna da kayayyakin lantarki, wadanda suka kasance tamkar ginshiki wajen raya masana'antun kasar Sin. Dalilin da ya sa Amurka ta yi binciken shi ne domin hana kasar Sin ta raya masana'antu mai ruwa da tsaki na zamani. (Tasallah Yuan)