Kakakin ya bayyana cewa, Sin ta dakatar da wasu ayyuka na baiwa kasar Amurka gatanci a cinikayyar da ke tsakaninsu, shi dai hakkin kasar Sin a matsayin memban hukumar WTO ne. A ranar 26 ga watan Maris ne, kasar Sin ta gabatar da bukatun yin shawarwari da kasar Amurka game da matakan ban gishiri in ba ka manda bisa yarjejeniyar matakan bada tabbaci ga ciniki, amma kasar Amurka taki amincewa. Sakamakon gaza cimma daidaito a tsakaninsu, Sin ta gabatar da jerin kayayyayin da take shigowa daga Amurka wadanda za ta dakatar da rangwame a kansu ga hukumar WTO, inda ta tsaida kudurin kara haraji kan kayayyakin don daidaita hasarorin da aka samu yayin da kasar Amurka ta dauki matakin mai lamba 232.
Kakakin ya kara da cewa, a matsayin manyan kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya, ya kamata Sin da Amurka su yi hadin gwiwa, da warware matsalolin ta hanyar yin shawarwari, da samun bunkasuwa tare don magance kara kawo illa ga yanayin hadin gwiwarsu a nan gaba. (Zainab)