Yau Talata ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya sake amsa tambayoyin manema labaru game da matsalar ciniki a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, inda ya jaddada cewa, idan wani bangare ya yi yunkura bullo da yakin ciniki, a nata bangare kasar Sin ba za ta ja da baya ba. Amma duk da haka, kasar Sin na bude kofarta ga yin shawarwari.
Ya ce ya zama tilas a tattauna, tare da gudanar da shawarwari bisa ka'idar girmama juna, da tabbatar da zaman daidai wa daida tsakanin dukkanin sassan biyu. (Tasallah Yuan)